Bikin ƴan kabilar Oromo da mai agoguna cikin hotunan Afrika na mako

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga cikin kayatattun hotunan Afrika na mako.

Masu rajin kare muhalli na kungiyar Extinction Rebellion Cape Town, a Afurka ta Kudu, su na wakiltar Afurka wadda ke cike da barazanar hayaki mai gurbata muhalli, sanye da tufafin lauyoyi da kawunan jarkokin mai da akai wa zane mai ban tsoro. An gudanar da babban taron a ranar Talata, makon man fetur na Afurka.

Asalin hoton, RODGER BOSCH / AFP

Bayanan hoto, Cike da fatan nasara ta hanyar amfani da wasan kwaikwayo, masu shirya wasan barkwanci suna nuna yadda gurɓataccen hayaki ke gurɓata muhalli. Sun yi amfani da jarkokin mai a matsayin fuskarsu, da tufafi launin fari da baki, inda suke tsorata matar da ke zaune, wadda ita ce ke wakiltar duniya. An ɗauki wannan lokacin taron koli kan yadda za a rage hayaki mai gurɓata muhalli.
Wannan dan kasuwar a birnin Alkhahira na Masar, ya baza hajarsa ta agoguna domin saidawa.

Asalin hoton, Khaled DESOUKI / AFP

Bayanan hoto, Lokaci na da muhimmanci, shi ya sa mallakar agogo ke karawa lokaci armashi.
Wani mai kada kuri’a a kasar Tunusia kenan yad anna yatsansa domin zabar jam’iyyar da yak e so a zaben shugaban kasa da aka yi a kasar Tunusia a ranar Lahadi .

Asalin hoton, FETHI BELAID / AFP

Bayanan hoto, An gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Tunusia a ranar Lahadin karshen mako
Wata mace sanye da abin adon mata da aka yi da duwatsu masu launi daban-daban a wurin bikin gargajiya mai suna Irreecha da ake yi a Hora Arsadi a Bishoftu.

Asalin hoton, TIKSA NEGERI / REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, mutane sun taru a tsakiyar garin Bishoftu na kasar Habasha
Women dressed in traditional Oromo costumes attend the Irreecha celebration, the Oromo people's thanksgiving festival at Hora Arsadi.

Asalin hoton, TIKSA NEGERI / REUTERS

Bayanan hoto, Rana ce da ake gudanar da gagarumin bikin godiya ga Allah ta ‘yan kabilar Oromo
Mazan kabilar Oromo lokacin bikin 'Irreecha' a Addis Ababa.

Asalin hoton, Michele Spatari / AFP

Bayanan hoto, Maza sun sha ado domin halartar bikin a birnin Addis Ababa...
'Yan kabilar Oromo na watsawa juna ruwa

Asalin hoton, Michele Spatari / AFP

Bayanan hoto, Wata al’ada ce ta cire ciyawa da furanni a kuma zuba a cikin ruwa domin godiya ga Allah da suke kira da sunan Waaqa, saboda albarkar damuna da aka samu, wannan buki shi ne yak e kawo karshen damuna a wannan shekara.
Ya na rike da gwal din da ya ke wankewa da kumfa

Asalin hoton, FRANCIS KOKOROKO / REUTERS

Bayanan hoto, Wani mutum na wanke shunkun gwal, a lokacin da ya ke aiki a wata masana’antar kere-kere a ƙasar Ghana.
Wani mutum cikin kwale-kwale ya na rat6sa unguwannin da ke gundumar Tougoude, a kudu maso yammacin birnin Ndjamena da kogin Logone ya haddasa ambaliyar ruwa.

Asalin hoton, JORIS BOLOMEY / AFP

Bayanan hoto, A dai wannan ranar ta Litinin, wannan mutumin a birnin N’djamaina na kasar Chadi, yana amfani da kwale-kwale saboda ba shi da wani zaɓi sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta a kudu maso yammacin kasar, musamman gundumar Tougoude
Mambar al'umar Chagossia, lokacin da suka yi dafifi a kofar majalisar dokokin Birtaniya a birnin Landan.

Asalin hoton, ADRIAN DENNIS / AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin 'yan tsiburin Chagos da ke zaune a Birtaniya, sun yi watsi da sanarwar gwamnatin kasar kan matakin karɓe iko da tsibirin da ke Mauritius - inda suke zanga-zangar lumana kan rashin tuntuɓarsu kan matakin da suka ce ya shafe su kai-tsaye
Ta na da tsahon mita 12, kuma kwararren mai kere-kere Ruffin Rakotomalala ne ya yi ta.

Asalin hoton, ZO ANDRIANJAFY / REUTERS

Bayanan hoto, Can a birnin Antananarivo na Madagascar, a dai ranar ta Litinin an dasa wannan doguwar gadar mai kama da ta kasar Faransa wato Eiffe
Wani Kyarkeci kenan ya ke gudu, a wani bangare na girmamawa ga shugaban kasar Mauritania da ke ziyara a fadar Bellevue a birnin Berlin.

Asalin hoton, FILIP SINGER / EPA

Bayanan hoto, A karshe sai kuma kasar Mauritania, inda shugaban kasar Mohamed Ould Ghazouani, kenan a fadar Bellevue ta kasar Jamus a ranar Talata.