Ƴan Man City bakwai ne ke takarar fitattu 11 na Fifpro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Manchester City bakwai ne daga 11 masu buga Premier League da ke takarar fitattu 11 na Fifpro 2024.
Real Madrid ce kan gaba mai yawan ƴan wasa takwas, harda ɗan ƙwallon Faransa, Kylian Mbappe, wanda ya koma Sifaniya daga Paris St Germain kafin fara kakar bana.
Ƴan wasan City da ke takara sun haɗa da mai tsaron raga, Ederson da mai tsaron baya, Ruben Dias da Kyle Walker da mai buga wasan tsakiya, Rodri da Kevin de Bruyne da Phil Foden da kuma Erling Haaland.
Cole Palmer yana ciki a karon farko a matakin ɗan wasan Manchester City da na Chelsea, wanda ya koma Stamford Bridge a Agustan 2023.
Ɗan wasan Bayern Munich, Harry Kane da na Real Madrid, Jude Bellingham suna daga cikin ƴan wasan Ingila daga 26 da ke takara.
Mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez yana cikin ƴan takara, amma ba sunan ɗan wasan tawagar Masar da Liverpool, Mohamed Salah daga cikinsu.
Ɗan wasan tawagar Argentina da Inter Miami, Lionel Messi da na Portugal da Al Nassr, Cristiano Ronaldo sune biyun da ba daga Turai ke taka leda ba daga 26 da aka bayyana.
Wannan shi ne karo na 18 da Messi ke shiga cikin ƴan takara a matakin kan gaba a yawan takara, sai Ronaldo mai 16.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙwararrun ƴan wasa ne ke yin zaben gwarzon ƴan kwallo 11 na Fifpro a kowacce kakar tamaula.
Fifpro ta sanar da cewar sama da ƴan wasa 21,000 daga kasa 70 suka kaɗa kuri'a.
Za a bayyana ƴan wasa 11 na Fifpro na bana a bikin da Fifa za ta gudanar na Fifa Best ranar 9 ga watan Disamba.
Jerin masu takarar Fifpro 11 na 2024
Masu tsare raga: Ederson (Manchester City, Brazil), Emiliano Martinez (Aston Villa, Argentina), Manuel Neuer (Bayern Munich, Germany)
Masu tsare baya: Dani Carvajal (Real Madrid, Spain), Ruben Dias (Manchester City, Portugal), Virgil van Dijk (Liverpool, Netherlands), Jeremie Frimpong (Bayer Leverkusen, Netherlands), Antonio Rudiger (Real Madrid, Germany), William Saliba (Arsenal, France), Kyle Walker (Manchester City, England)
Masu buga tsakiya: Jude Bellingham (Real Madrid, England), Kevin de Bruyne (Manchester City, Belgium), Phil Foden (Manchester City, England), Toni Kroos (Real Madrid, Germany), Luka Modric (Real Madrid, Croatia), Jamal Musiala (Bayern Munich, Germany), Rodri (Manchester City, Spain), Federico Valverde (Real Madrid, Uruguay)
Masu cin ƙwallaye: Erling Haaland (Manchester City, Norway), Harry Kane (Bayern Munich, England), Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain/Real Madrid, France), Lionel Messi (Inter Miami, Argentina), Cole Palmer (Manchester City/Chelsea, England), Cristiano Ronaldo (Al-Nassr, Portugal), Vinicius Jr (Real Madrid, Brazil), Lamine Yamal (Barcelona, Spain)










