Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashford da Henderson ba sa cikin ƴan Ingila na kwarya-kwarya
Marcus Rashford da Jordan Henderson ba sa cikin ƴan wasan Ingila 33 na ƙwarya-ƙwarya da Gareth Southgate ya bayyana don buga Euro 2024.
Ɗan ƙwallon Manchester United, Rashford, mai shekara 26, bayan kan ganiya, wanda ya ci ƙwallo bakwai ya bayar da biyu aka zura a raga a wasa 33 a lik.
Ya buga wa tawagar Ingila wasa bakwai a bana daga baya ba a gayyace shi ba karawa da Belgium a cikin watan Maris.
Henderson ya koma taka leda a Al-Ettifaq ta Saudi Arabia daga Liverpool a bara, amma daga baya ya koma Ajax a watan Janairu.
Southgate ya ci gaba da gayyatar Henderson tun bayan da ya koma buga tamaula a Saudi Arabia, amma wasu magoya bayan Ingila sun yi masa ihu a karawa da Australia cikin watan Oktoba a Wembley.
An gayyaci Henderson tawagar Ingila a wasan sada zumunta a cikin watan Maris da Brazil da kuma Belgium, amma bai buga wasannin ba.
Nan gaba Southgate zai fitar da ƴan wasa bakwai daga cikin tawagar su koma 26 kafin 7 ga watan Yuni.
Ƴan wasan tawagar Ingila na ƙwarya-ƙwarya:
Masu tsare raga: Dean Henderson (Crystal Palace), Jordan Pickford (Everton), Aaron Ramsdale (Arsenal), James Trafford (Burnley).
Masu tsare baya: Jarrad Branthwaite (Everton), Lewis Dunk (Brighton), Joe Gomez (Liverpool), Marc Guehi (Crystal Palace), Ezri Konsa (Aston Villa), Harry Maguire (Manchester United), Jarell Quansah (Liverpool), Luke Shaw (Manchester United), John Stones (Manchester City), Kieran Trippier (Newcastle), Kyle Walker (Manchester City)
Masu buga tsakiya: Trent Alexander-Arnold (Liverpool), Conor Gallagher (Chelsea), Curtis Jones (Liverpool), Kobbie Mainoo (Manchester United), Declan Rice (Arsenal), Adam Wharton (Crystal Palace).
Masu cin ƙwallaye: Jude Bellingham (Real Madrid), Jarrod Bowen (West Ham), Eberechi Eze (Crystal Palace), Phil Foden (Manchester City), Jack Grealish (Manchester City), Anthony Gordon (Newcastle), Harry Kane (Bayern Munich), James Maddison (Tottenham), Cole Palmer (Chelsea), Bukayo Saka (Arsenal), Ivan Toney (Brentford), Ollie Watkins (Aston Villa).