Liverpool za ta buga Champions League duk da tashi 3-3 da Villa

An wallafa

Liverpool ta samu gurbin shiga Champions League a badi, bayan da ta tashi 3-3 a wasan mako na 37 a Premier League a Villa Park ranar Litinin.

Aston Villa ce ta fara cin gida ta hannun mai tsaron raga, Emiliano Martinez a minti na biyu da take leda, daga baya ta farke ta hannun Youri Tielemans.

Ƙwallon da Martinez ya ci gida shi ne gola da ya ci gida a kankanin lokaci a Premier League, bayan tarihin mai tsaron ragar Everton, Antolin Alcaraz a wasa da Southampton cikin Afirilun 2014.

Karo na uku da Martinez ya ci gida a tarihin Premier League, kuma shi ne kan gaba a matakin mai tsaron raga da ya ci gida da yawa a gasar.

Bayan da wasan ke nutsuwa ne Liverpool ta kar na biyu ta hannun Cody Gakpo, kuma haka suka je hutu kungiyar Anfield ta ci 2-1.

Ƙwallon da Gakpo ya zura a raga shi ne na 1,196 a Premier League a 2023-24, wato kaka ta biyu da aka dura kwallaye da yawa a raga bayan 1992-93 da aka ci 1,222.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Liverpool ta kara na uku ta hannun Jarell Quansah.

Daga baya Aston Villa ta kara sa kaimi ta zare ta biyu ta hannun Jhon Duran, sannan ya farkewa Villa na uku saura minti biyar a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 79 ta kuma samu gurbin shiga Champions League a badi tana ta ukun teburi, saura wasa daya a kare kakar nan.

Liverpool, wadda ta kara a Europa League a kakar nan ta yi ban kwana da wasannin gasar, bayan da Atalanta ta fitar da ita.

Aston Villa mai fatan wakiltar Ingila a gasar zakarun Turai ta badi, wadda take da maki 68 a mataki na hudu na bukatar cin wasan karshe, bayan da Tottenham ke biye da ita ta biyar da maki 63 da wasa biyu a gabanta.

Aston Villa ta yi waje daga Conference League na bana, bayan da Olympiacos ta yi nasara a zagayen daf da karshe.

Ranar Lahadi 19 ga watan Mayu za a buga wasan karshe a Premier na bana, inda Aston Villa za ta je Crystal Palace a Selhurst Park.

Ita kuwa Liverpool, wadda Jurgen Kloop ya ja ragamar cin wasa 298 a kungiyar, za ta karbi bakuncin Wolverhampton a Anfield.

Da zarar an kammala kakar bana Kloop zai yi ban kwana da Liverpool, zai je ya huta, bayan shekara tara a kungiyar.

Jerin wasu batutuwan da ya kamata ku sani:

Wasa daya Aston Villa ta yi nasara daga karawa 10 da canjaras daya a fafatawa 12 a Premier League da ta fuskanci Liverpool. Shi ne wanda ta ci 7-2 win at Villa Park a cikin Oktoban 2020.

Liverpool ta yi nasara da yawa a wasan Premier League da take zuwa gidan Aston Villa da cin wasa 16.

Liverpool ta yi nasara a kan Newcastle da West Ham sau 35 kowacce sai kuma Aston Villa wasa 33.

Wasa daya Livepool ta yi rrashin nasara daga 26 da ta yi a Premier League cikin watan Mayu mai nasara 19 da canjaras shida.

Mohamed Salah ya ci kwallo ya kuma bayar an zura a raga karo na hudu a kakar nan a Premier League, wanda ke gabansa a wannan bajintar shi ne Cole Palmer na Chelsea mai biyar.

Kenan Salah shi ne na uku a wannan kwazon da ya yi karo 31, mai biye da shi kuwa shi ne Thierry Henry mai 32 da kuma Wayne Rooney mai 36.