Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Napoli za ta ɗauki McTominay ɗan wasan Man United
Napoli ta amince da farashin £25.4m da Manchester United ta sallamar, domin sayen Scott McTominay.
Koda yake ba a kai ga cimma mikawa ɗan wasan ƙunshin kwantiragi ba, domin ya koma taka leda a Gasar Serie A, amma dai kiris ya rage.
Tun a farkon watan Agusta, United ta ƙi sallama tayin £20m da Fulham ta yi, domin ɗaukar ɗan wasan tawagar Scotland.
Dan wasan mai shekara 27 ya yi watsi da tayin komawa taka leda a West Ham a bara, daga baya ya ci gaba da yi wa United tamaula da cin ƙwallo bakwai a wasa 32 a Premier League.
Haka kuma McTominay yana cikin waɗanda suka fara buga wa United FA Cup karawar karshe a watan Agusta a Wembley, inda Manchester City ta lashe kofin.
Da yake Napoli ta nuna sha'awar sayen ɗan wasan a bana, hakan ya sa ba a fara wasan United biyu da shi ba, wanda ke zaman benci daga baya a saka shi a wasan.
Har yanzu koci, Erik ten Hag na fatan kara karfin United kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo ta Turai zuwa karshen watan nan.
United tana ta kokarin sayen ɗan wasan tawagar Uruguay, mai taka leda a Paris St-Germain, Manuel Ugarte.
Ranar Asabar United ta yi rashin nasara 2-1 a wasan mako na biyu a Premier League a gidan Brighton a filin wasa na Amex.