Rodrygo ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2028 a Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na Brazil Rodrygo ya rattaɓa hannu kan sabuwar yarjejeniya da Real Madrid har zuwa shekarar 2028 tare da sharaɗin duk ƙungiyar da za ta ɗauke shi a cikin wannan lokaci sai ta biya Yuro Biliyan ɗaya.
Ɗan wasan mai shekara 22 ya ci ƙwallaye 39 a wasanni 179 da ya buga wa Real sannan kuma ya buga wa Brazil wasanni 18.
Ɗan wasan ya koma kulob din La Liga yana da shekaru 18 daga Santos ta Brazil.
A zamansa a Real ya lashe kofunan La Liga biyu, da Copa del Rey, da Champions League da Uefa super cup da kuma kofin duniya na ƙungiyoyi.
An saka shi cikin tawagar Brazil ta gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ya buga wasanni biyar a Qatar.
Abokin wasan Rodrygo na ƙasa da ƙasa Vinicius Jr shi ma ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din har zuwa shekarar 2027 a farkon makon nan.





