United ta kara yin tuntube a wasa na biyu a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta ci karo da koma baya, sakamakon doke ta 3-2 da Galatasaray ta yi a wasa na bibiyu a cikin rukuni a Champions League.
United ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Rasmus Hojlund a minti na 17 da fara tamaula, amma minti shida tsakani tsohon dan wasan United Wilfried Zaha ya farke.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta kara ta hannun, Rasmus Hojlund, sai dai mintunan ba yawa Galatasaray ta farke ta hannun Kerem Akturkoglu.
Mauro Icardi ne ya ci wa Galatasaray kwallo na uku, wanda tun kan nan ya barar da fenariti.
Kungiyar Old Trafford ta karasa wasan da ''yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Casemiro jan kati.
Karon farko da dan kwallon United ya karbi jan kati a Champions League tun bayan wanda aka kori Wan Bissaka a wasa da Young Boys ranar 14 ga watan Satumbar 2021.
Daya wasan rukunin farko kuwa Bayern Munich ce ta je ta yi nasara a gidan FC Copenhagen da ci 2-1.
Wannan shi ne wasa na bakwai da suka kece raini a tsakaninsu, inda kungiyar Turkiya ta yi nasara ta biyu, United ma biyu ne da ita da canjaras uku.
A karashen mako United ta yi rashin nasara a hannun Crystal Palace da ci 1-0 a karawar mako na bakwai a gasar Premier League ranar Asabar.
United wadda take ta 10 a teburin Premier League za ta karbi bakuncin Brentford ranar Asabar 7 ga watan Oktoba, sannan ta je gidan Shiffield United ranar 21 ga watan nan.
Daga nan United za ta karbi bakuncin FC Kopenhagen a fafatawa ta uku-uku a cikin rukuni a Champions League.












