Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihi da yawa aka kafa bayan cin Man United 7-0
An wallafa
Liverpool ta sharara kwallo 7-0 a ragar Manchester United a wasan mako na 26 a gasar Premier League a Anfield ranar Lahadi.
Liverpool ta ci kwallo biyu ta hannun Cody Gakpo da Darwin Nunez shima biyu ya zura a raga, Mohamed Sala ya ci biyu, sannan Ferminho ya zura na bakwai.
Ga jerin tarihin da aka kafa ranar Lahdi a Anfield:
- Mohamed Salah ya zama na farko a Liverpool da ya ci Manchester United kwallo a wasa shida a jere a dukkan fafatawa.
- Dan kasar Masar, ya zama kan gaba a Liverpool a yawan cin kwallaye a Premier League a tarihi mai 129 a wasa 205.
- Cody Gakpo da Darwin Núñez sun zama na farko a Liverpool da suka zura kwallo bibiyu a ragar United a kaka daya tn bayan bajintar da Arthur Goddard da James Stewart suka yi a Fabrairun 1910.
- Karon farko da Liverpool ta ci United kwallo da yawa a tarihin haduwar da suke yi, kungiyar Anfield ta taba cin ta Old Trafford 7-1 a Oktoban 1895 a gasar rukuni na biyu.
- An kawo karshen wasa 12 da United ta buga a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba, tun bayan 3-2 da Arsenal ta yi mata a Janairun 2023.
- Bayan da aka ci United 7-0, shine wasan da aka zura kwallo da yawa karkashin Erik ten Hag tun bayan da ya fara horar da tamaula, ya ja ragamar United karo na 48 ranar Lahadi.
- Wasan da aka ci United kwallaye da yawa a tarihi tun bayan shekara 92 kuma na waje a tarihi da kwallao da yawa ya shiga ragarta.
- Karo na hudu da aka taba doke United 7-0 kenan, bayan wanda Wolves ta yi nasara a Disambar 1931 da na Aston Villa a Disambar 1930 da kuma Blackburn Rovers a Afirilun 1926.