Van Dijk na tattaunawa da Liverpool kan tsawaita kwantarginsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ya tabbatar da cewa yana tattaunawa da ƙungiyar domin tsawaita kwantaraginsa.

Mai shekara 33 ya koma Anfield ne a 2018 kuma kwantaraginsa za ta ƙare ne a ƙarshen wannan kakar.

"Muna ci gaba da tattaunawa, za mu ga mai zai faru nan gaba," in ji ɗan wasan bayan Netherland ɗin.

"Duka tunina yana kan Liverpool, ina son samun nasraa kan wasannin da ke gabanmu bayan nan ba wani abu.

"Me zai faru a nan gaba, ni ma ban sani ba. Zan dai iya tabbatar muku da cewa muna tattaunawa abin da zai faru kuma nan gaba za mu gani."

Dan wasan Ingila Trent Alexander-Arnold da na Masar Mohamed Salah kwantaraginsu za ta ƙare a kaka mai zuwa, kuma babu wani bayani kan sabunta kwantaragin na su.

Liverpool ta ɗauki ɗan wasan ne daga Southampton kan kuɗi fan miliyan 75, ya kuma taimaka mata ta lashe Premier da Champions da FA da Fifa Club World Cup.

Ƙarƙashen sabon kocin Liverpool ɗan ƙasar Netherland Arne Slot, Van Dijk ya taimaka wa Liverpool tana matsayi na ɗaya a gasar Premier a wannan kakar, kuma sun ci wasa bakwai cikin takwas da suka buga a wannan kakar.

"Ina jin daɗi, a jikina da kuma kwakwalwata ina farin ciki," in ji Van dijk, wanda ya tattauna da 'yan jarida bayan nasarar da suka yi kan Chelsea 2-1.

"Lokacin da ya kamata a yanke hukunci zai zo, kuma za mu faɗa muku."

Van Dijk yana taiamakwa Liverpool wadda aka ci kwallo uku kacal a wannan shekarar, kuma shi ne ɗan bayan da ba su taɓa irinsa ba a Premier.