Duran ya tsawaita zama a Villa zuwa karshen kakar 2030

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Aston Villa, Jhon Duran ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Villa Park har zuwa karshen kakar 2030.
Mai shekara 20 ya koma Villa Park da taka leda a Janairun 2023 kan £18m daga Chicago Fire mai buga gasar Amurka ta Major League Soccer.
Ya koma ƙungiyar da ke buga Premier League a lokacin kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen 2028, yanzu an kara masa kaka biyu kenan.
Kaɗan ya rage ɗan wasan tawagar Colombia ya bar Villa Park, bayan da Chelsea da kuma West Ham suka nuna sha'awar sayen ɗan wasan.
Daga baya ya ci gaba da taka leda a Villa, wanda kawo yanzu ya ci ƙwallo shida a bana, har da 1-0 da ya ci Bayern Munich a Champions League a makon jiya.
Haka kuma shi ne ya ci ƙwallon da Villa ta samu maki uku a kan West Ham da Leicester da kuma Everton a Premier League a kakar nan.
Ɗan wasan tawagar Colombia shi ne na biyu da Unai Emery ya saya a Villa Park, tun bayan da ya karɓi aikin horar da ita a Oktoban 2022.
Ya ci ƙwallo 14 a wasa 56 a Aston Villa da ɗaya da ya ci wa Colombia a karawa 12.










