Falasɗinawa sun yi zanga-zangar adawa da Hamas a Gaza

    • Marubuci, Rushdi Aboualouf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent
    • Marubuci, Alex Boyd
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ɗaruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da ƙungiyar Hamas a Gaza, wadda ta kasance zanga-zanga mafi girma tun bayan harin da ƙungiyar da tai wa Isra'ila a cikin watan Oktoban 2023.

Masu zanga-zangar sun buƙaci Hamas ta sauka daga mulkin yankin.

Sai dai wasu mayaƙan ƙungiyar ɗauke da bindigogi da sanduna, fuskokinsu a rufe sun tarwatsa masu zanga-zangar.

Bidiyon da masu fafutuka da ke sukar ƙungiyar ta Hamas suka yaɗa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda matasa suke yin tattaki a kan titunan birnin Beit Lahia, a arewacin Gaza, a ranar Talata suna ihun cewa Hamas ta fita.

Masu goyon bayan ƙungiyar sun kare ta, sun kuma nuna rashin tasirin zanga-zangar tare da kiran masu boren da cewa maciya amana ne.

Amma ita ƙungiyar ta Hamas ba ta ce komai ba.

Zanga-zangar ta zo ne kwana ɗaya bayan mayaƙan Hamas sun harba rokoki Isra'ila, lamarin da ya kai Isra'ilar yanke shawarar cewa a bar mafi yawa na ɓangaren birnin, Beit Lahia, kuma hakan ya janyo ɓacin ran jama'a.

Isra'ila ta dawo da kai hare-hare a Gaza ne bayan kimanin wata biyu da aka kwashe na tsagaita wuta, inda Isra'ilar ta ɗora wa Hamas laifi kan cewa ta ƙi amincewa da tayin Amurka na tsawaita yarjejeniyar.

Hamas a nata ɓangaren ta zargi Isra'ila da yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tun da farko a watan Janairu.

Ɗaruruwan Falasɗinawa ne aka kashe tun bayan da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-haren nata a Gaza a ranar 18 ga watan Maris.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, mazaunin Beit Lahia, Mohammed Diab, ya rasa gidansa da ɗan'uwansa a hare-haren Isra'ilar kan Gaza shekara ɗaya da ta gabata.

Ya ce "Ba mu son mu ci gaba da mutuwa, sanadiyyar ra'ayin wata jam'iyya ko kuma don biye wa wasu ƙasashen ƙetare".

"Wajibi ne Hamas ta sauka daga mulki kuma ta saurari muryoyin mutanen da suke cike da jimami, muryoyin mutanen da ke murƙushe a ƙarƙashin ɓaraguzai – ita ce murya mafi ƙarfi."

Hamas ce ke tafiyar da Gaza tun daga shekarar 2007 bayan zaɓen da ta lashe a 2006 tare da kawar da abokan hamayyarta.

Sukar lamirin Hamas na ci gaba da ƙaruwa a Gaza tun bayan da yaƙin ya ɓarke.

Dama akwai mutane masu adawa da Hamas tun kafin ɓarkewar yaƙin, sai dai mafi yawancinsu na yi ne a ɓoye don gudun farmaki.

Harin da Hamas ta kai a Isra'ila, ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ne ya kunna wutar ɓarkewar mummunan yaƙin na baya-bayan nan, inda a lokacin aka kashe Isra'ilawa kimanin 1,200, mafi yawan su fararen hula, sannan aka yi garkuwa da mutum 251.

Isra'ila ta mayar da martani da ruwan hare-hare ta sama da ta ƙasa a kan Gaza, lamarin da hukumar lafiya ta Hamas ta ce ya yi sanadin rayukan Falasɗinawa sama da 50,000.

Haka nan an tarwatsa akasarin mazauna yankin Gaza su miliyan 2.1 daga muhallansu.

An yi ƙiyasin cewa lamarin ya yi sanadin lalata kashi 70 cikin ɗari na gine-ginen da ke Gaza. Harkar kiwon lafiya da ruwan sha da tsaftar muhalli duk sun durƙushe, sannan ana cikin yanayi na ƙarancin abinci da magani da muhallin zama.