Yadda Kanawa ke gudanar da sana’o’insu a yanayin tsananin zafi
Yadda Kanawa ke gudanar da sana’o’insu a yanayin tsananin zafi
An wallafa
Kamar sauran akasarin biranen arewacin Najeriya, mazauna Kano na ci gaba da fama da zafin da ba a saba ganin irinsa ba.
Sai dai ganin yadda birnin ya shahara wajen hada-hadar kasuwanci da ayyukan hannu, haka mutane kan gudanar da harkokinsu a cikin zafin.
Wani makanike ya bayyana yake yawan jiƙa hularsa duk bayan mintuna don sauƙaƙa wa kansa zafin yayin da yake gudanar da aikinsa.
"Haka muke fitowa don mu samu abin da za mu kai bakin salati," in ji wani mai faskaren itace.



