Mikhail Gorbachev: Shugaban Tarayyar Soviet da ya kawo karshen yakin cacar-baka

Bayanan bidiyo, Shugaban Tarayyar Soviet da ya taimaka wajen kawo karshen yakin Cacar-Baka
Mikhail Gorbachev: Shugaban Tarayyar Soviet da ya kawo karshen yakin cacar-baka
An wallafa

Mikhail Gorbachev, tsohon shugaban Tarayyar Soviet wanda ya kawo karshen yakin Cacar-Baka, ya mutu yana da shekaru 91.

Mr Gorbachev, wanda ya karbi mulki a 1985, ya bai wa kasashen duniya damar yin hulda da Tarayyar kuma ya gabatar da sauye-sauye a cikin gida.

Jama'a a fadin duniya suna alhinin rasuwarsa, inda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce ya "sauya tsarin tarihi".