Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid na bukatar maki uku a kan Espanyol
Real Madrid za ta fafata da Espanyol ranar Asabar a wasan mako na 25 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.
A wasan farko a kakar bana, Real ce ta je ta ci Espanyol 3-1 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Real Madrid na bukatar hada maki uku a wasan, domin ta rage tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona, wadda sai a ranar Lahadi za ta yi wasanta.
Haka kuma kungiyar ta Santigo Bernabeu za ta buga karawar da zai ba ta karfin gwiwar fuskantar Liverpool a Champions League a Sifaniya.
Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Real da cin 5-2 a wasan farko a Anfield zagayen 'yan 16 a gasar zakarun Turai ta kakar nan.
Luca Modric zai buga wasan, wanda ya yi hukuncin dakatarwa wasa daya, bayan da ya karbi katin gargadi biyar.
To sai dai Carlo Ancelotti zai yi wasan ba tare da Alaba da Mendy da kuma Benzema ba, wadanda ke jinya.
Ancelotti ya tabbatar Rodrygo zai fara fuskantar Espanyol, wanda shi da Vinicius Jr suka taka rawar gani a sanadin cin kwallo 20 a La Liga a bana.
Espanyol, wadda take ta 13 a kasan teburin La Liga mai maki 27 ta ci wasa shida da canjaras tara aka doke ta karawa tara a kakar nan.
Koda yake kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Valladolid a wasan da ta kara, amma tana fatan cin karawa uku daga hudu a bayan nan a La Liga.
Dan wasan da yake da hadari a Espanyol, shine Joselu, wanda keda kwallo 11 a raga, shine ya zare dayan da Real ta ci 3-1 a wasan farko.