Waiwaye: Zaɓen shugabannin majalisa, dakatar da shugaban EFCC

An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

Akpabio da Tajuddeen sun zama shugabannin majalisar Najeriya ta 10

A ranar Talatar makon da ya gabata ne majalisar dokokin Najeriya ta 10 ta sabi sabbin shhugabannin da za su jagoranci majalisar.

An zaɓi Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibril, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da mataimakinsa.

Godswill Akpabio ya ci zaɓen ne da ƙuri'a 63 a kan abokin takararsa Sanata Abdul'aziz Yari wanda ya samu ƙuri'a 46.

A majalisar wakilan ƙasar kuma an zaɓi Hon. Tajuddeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu, a matsayin shugaba da mataimakin shugaban majalisar wakilan.

A lokacin zaɓen 'yan majalisar wakilai 353 ne suka kaɗa ƙuri'unsu ga Tajuddeen Abbas.

Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC

Haka kuma a farkon makon da muke bankwana da shi ɗin ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon Ƙasa EFCC AbdulRasheed Bawa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya ta ce shugaban ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ake yi wa Bawa.

Sanarwar, daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ya sanya wa hannu, ta ce an bai wa AbdulRasheed Bawa umurnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.

Ina neman afuwar Musulmai kan kalamaina – Kashim Shettima

Haka kuma a cikin makon ne maitamakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya bayyana neman afuwar al'ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaɓen shugabannin majalisar dokokin Najeriya.

A cewarsa ba a fahimci maganar a muhallinta ba, kuma ba shi da wata manufa na ɓata sunan addininsa.

Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi waɗannnan kalamai ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama'a yana bayani a kansu ba.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ''Ina neman gafarar musulmi da afuwar ubangiji kan kalaman da na yi, amma ban yi su da nufin cutar da addini ba''.

Kotu ta umarci DSS su bar Emefiele ya ga iyalansa

A ranar Juma'a ne kuma babar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar DSS din kanta da su gaggauta bai wa gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda tsarin mulki ya tanadar.

Lauyan Emefiele JB Daudu ya sanar da kotun cewa ya rubuta wa hukumar DSS wasiku, musamman a ranar 14 ga watan Yuni domin neman ƙarin umarni daga wurinsa, amma hukumar DSS ta ƙi amsa buƙatar.

A ɗaya ɓangaren kuma lauyan waɗanda ake ƙara na biyu da na uku, I. Awo, ya shaida wa kotun cewa hukumar DSS ba ta da hurumin ƙin amincewa da wannan buƙata, kuma yin hakan ba daidai ba ne.

Kotu ta umarci ƴansanda su mayar da kayan da suka kwashe daga gidan Matawalle

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Gusau ta umarci rundunar ‘yan sandan Najeriya da wasu hukumomi hudu da ke da hannu wajen kwashe motoci da sauran kayayyaki daga gidajen tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da su mayar da su cikin sa’o’i 48.

A ranar 9 ga watan Yuni ne ‘yan sanda tare da jami’an DSS da NSCDC suka kai samame a gidajen tsohon gwamnan a Gusau da Maradun inda suka yi awon-gaba da motoci da wasu kayan gwamnan da na iyalansa bisa umarnin wata karamar kotu.

Daga baya a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta kwato motoci 40 a lokacin samamen amma ta yi shiru kan sauran kayan da tsohon gwamnan ya yi zargin an kwashe.