Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United za ta iya komawa kan ganiyarta - Van Nistelrooy
Manchester United na iya komawa kan ganiyarta amma zai ɗauki lokaci da aiki tukuru, in ji kocin rikon ƙwarya Ruud van Nistelrooy.
Tsohon ɗan wasan na United da Netherlands zai fara jagorantar ƙungiyar a karon farko a wasan da Leicester City za ta ziyarci Old Trafford a zagayen ƴan 16 a gasar cin kofin Carabao a ranar Laraba.
An sanya shi a matsayin kocin wucin gadi bayan korar Erik Ten Hag a ranar Litinin, inda United ke matsayi na 14 a gasar Premier.
United ta tuntuɓi kocin Sporting Ruben Amorim, kodayake a ranar Talata ya ce bai yanke shawara kan makomarsa ba.
Van Nistelrooy ya shafe shekara biyar a United a matsayin ɗan wasa daga 2001 zuwa 2006, inda ya lashe Kofin Firimiya da Kofin FA, da EFL Cup da kuma FA Community Shield.
Tsohon ɗan wasan gaban ya koma kulob ɗin a bazara, inda ya kasance mataimakin Ten Hag.
"Lokacin da na dawo a lokacin bazara a matsayin mataimakin Erik, na yi imani ne cewa Manchester United za ta iya komawa matakin da na sani lokacin da ne ke ɗan wasa," in ji Van Nistelrooy.
"Har yanzu ina da wannan yaƙinin, amma zai ɗauki lokaci da kuma aiki tuƙuru.''
Babu tabbas ko zai ci gaba da zama a kulob ɗin idan aka naɗa sabon kocin dindindin inda a halin yanzu aka ce United ta tuntuɓi Ruben Amorin na Sporting Lisbon.