Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta gwada wa Las Palmas ƙwanji a La Liga
Real Madrid ta sharara ƙwallaye a ragar Las Palmas da cin 4-1 a La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu, karawar mako na 20.
Minti ɗaya da take wasa Las Palmas ta zura ƙwallo ta hannun Fábio Silva daga baya Kylian Mbappe ya farke a bugun fenariri, sannan ya kara na biyu.
Sauran da suka ci wa Real ƙwallayen a wasan sun hada da Brahim Díaz da kuma Rodrygo da ta kai ta haɗa maki ukun da take bukata.
To sai dai Las Palmas ta karasa karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, sakamakon da aka bai wa Benito Ramírez jan kati a minti na 64.
Ranar 29 ga watan Agustan 2024, Real Madrid ta je ta tashi 1-1 a gidan Las Palmas a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Da wannan sakamakon Real Madrid tana ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 46, bayan karawar mako na 20.
Atletico Madrid ce ta biyu da maki 44 da kuma Barcelona ta uku mai maki 39.
Ranar Laraba 22 ga watan Janairu, Real Madrid za ta karɓi bakuncin RB Salzburg a Champions League daga nan ta je Valladolid a La Liga ranar Asabar 25 ga Janairu.