Kungiyoyi biyar na harin Semenyo, Everton na son ɗauko Hackney

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal, da Liverpool, da Manchester City, da Manchester United sannan Tottenham na harin ɗan wasan Bournemouth mai shekaru 25 Antoine Semenyo, da ƙungiyarsa ta shirya siyar da shi kan fam miliyan 65, inda aka buɗe kakar siyen ƴan wasa a watan Janairu. (Talksport)

Manchester United za ta iya sallama ɗan wasanta Joshua Zirkzee, da Roma ke son ɗauka, domin samun damar siyen Semenyo. (Mail - subscription required)

Ɗan wasan Chelsea Tyrique George zai bar ƙungiyar a watan Janairu, yayin da ƙungiyoyi da ke buga Premier League, tare da RB Leipzig da Roma, ke son ɗaukar ɗan wasan, mai shekaru 21. CaughtOffside)

Everton na son ɗuko ɗan wasan Middlesbrough Hayden Hackney sai dai za su yi gwagwarmaya wajen ganin ɗan wasan ya tsaiwata kwantaraginsa, a watan Janairu, sakamakon Boro na ƙalubalantar neman ƙara ciyar da shi gaba a gasar. (Teamtalk)

Aston Villa na shirye shiryen fara tattaunawa kan Youri Tielemans, 28, don tsawaita kwantaraginsa, idan kwantaragin tasa ta ƙare a 2028. (Football Insider)

West Ham ta ce za ta sallami Niclas Fullkrug, yayin da AC Milan zata iya ɗaukar ɗn wasan a masatyin aro a Janairu. (Guardian)

AC Milan za ta iya biyan wani albashi na wucin gadi ga Fullkrug, da ya kai kusan fam dubu ɗari duk sati, sai dai ta ce za ta sake yin duba a kan kwataragin don mayar da zamansa na dundundun. (Givemesport)

Juventus ana harin ɗan wasan Marseille Pierre-Emile Hojbjerg, sai dai ƙungiyar na son ci gaba da riƙe ɗan wasan ɗan asalin Denmark. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Arsenal za su ɗauko ɗan wasan AC Milan mai shekaru 19 Davide Bartesaghi, da kwantaraginsa zata ƙare a 2030. (Calciomercato - in Italian)

Manchester United ta sake sabunta kwantaragin ɗan wasan Trabzonspor Christ Inao Oulai. Su ma Manchester City na son ɗaukar ɗan wasan. (Teamtalk)

Aston Villa ba za ta siyar da ɗan wasan ta Lamare Bogarde, duk da son ɗaukarsa da Brighton ke yi. (Football Insider)

Inter Miami na matakin ƙarshe na baiwa Luis Suarez tsawita zamansa a ƙungiyar don takawa ƙungiyar leda a gasar wasannin 2026. (Athletic - subscription required)