Fadar Fir'auna da ambaliyar ruwa a sahara cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Mai kula da wannan wajen na ibada kenan Abdel Karim, yake maraba da baƙin da suka je kallon yadda rana ke haska gunkin mutum-mutumin Fir’auna (Ramses) na biyu a Masar a ranar Talata. Sau biyu kawai a shekara hasken ranar ke yin haka

Asalin hoton, FAREED KOTB/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mai kula da wannan wurin na ibada kenan Abdel Karim, yake maraba da baƙin da suka je kallon yadda rana ke haska mutum-mutumin Fir’auna (Ramses) na biyu a Masar a ranar Talata. Sau biyu kawai a shekara hasken ranar ke yin haka
A ranar Litinin magoya bayan jam'iyya mai mulki a Kamaru suka yi dafifi domin tarbar shugaban ƙasar mai shekara 91, wanda aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa ya rasu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin magoya bayan jam'iyya mai mulki a Kamaru suka yi dafifi domin tarbar shugaban ƙasar mai shekara 91, wanda aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa ya rasu.
Wata mata da yarinya suna saƙa kwando a lokacin wani bikin al'ada a birnin Ghadames na Libya ranar Laraba...

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA/AFP

Bayanan hoto, Wata mata da yarinya suna saƙa kwando a lokacin wani bikin al'ada a birnin Ghadames na Libya ranar Laraba...
Masu kiɗan Mandiri

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA/AFP

Bayanan hoto, An sha kaɗe-kaɗe ma a lokacin bikin al'adar na Libya
Waɗannan yaran 'yan matan sun caɓa ado a lokacin bikin al'adar a Libya

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA/AFP

Bayanan hoto, Waɗannan yaran 'yan matan sun caɓa ado a lokacin bikin al'adar a Libya
Tarin na'urorin tarho na daga cikin kayayyakin da aka rataye a bango a cibiyar shirya fina-finai ta Atlas Studios da ke birnin Ouarzazate na Morocco a ranar Litinin

Asalin hoton, WILFRID ESTEVE/HANS LUCAS/AFP

Bayanan hoto, Tarin na'urorin tarho na daga cikin kayayyakin da aka rataye a bango a cibiyar shirya fina-finai ta Atlas Studios da ke birnin Ouarzazate na Moroko a ranar Litinin.
Wasu matasan mabiya addinin Buda kenan da suka yi layi za su karɓi hadaya daga al'ummar garin Entebbe a Uganda a lokacin bikukuwan addini na Kathina

Asalin hoton, BADRU KATUMBA/AFP

Bayanan hoto, Wasu matasan mabiya addinin Buda kenan da suka yi layi za su karɓi hadaya daga al'ummar garin Entebbe a Uganda a lokacin bikukuwan addini na Kathina
Wannan lokaci ne na atisaye na jirgin sama na leda (irin na yara), ranar Talata a Cape Town, kafin gasar duniya da za a yi ta jirgin

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Wannan lokaci ne na atisaye na jirgin sama na leda (irin na yara), ranar Talata a Cape Town, kafin gasar duniya da za a yi ta jirgin
Waɗannan matan sun je Afirka ta Kudu ne tun daga Tunisia domin shiga gasar ta shekara-shekara, wadda ake tara kuɗi domin taimaka wa masu matsalar ƙwaƙwalwa.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Waɗannan matan sun je Afirka ta Kudu ne tun daga Tunisia domin shiga gasar ta shekara-shekara, wadda ake tara kuɗi domin taimaka wa masu matsalar ƙwaƙwalwa.
Masu wasan kwaikwayo a lokacin wani biki na taron kan iyaka na Abidjan a Ivory Coast ranar Laraba.

Asalin hoton, LEGNAN KOULA/EPA

Bayanan hoto, Masu wasan kwaikwayo a lokacin wani biki na taron kan iyaka na Abidjan a Ivory Coast ranar Laraba.
Alamar ambaliyar watan da ya gabata a cikin Hamadar Sahara a kudu maso gabashin Moroko ranar Lahadi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Alamar ambaliyar watan da ya gabata a cikin Hamadar Sahara a kudu maso gabashin Moroko ranar Lahadi
Wannan makarantar da ambaliya ta mamaye a makon da ya gabata a Senegal har yanzu ruwan yana nan - ranar Talata

Asalin hoton, GUY PETERSON/AFP

Bayanan hoto, Wannan makarantar da ambaliya ta mamaye a makon da ya gabata a Senegal har yanzu ruwan yana nan - ranar Talata
Mata da yara 'yan Sierra Leone, waɗanda masu gidajen da suke yi wa aiki 'yan Lebanon suka kora sannan suka yi watsi da su bayan harin Isra'ila na neman mafaka a Beirut ranar Lahadi. 'Yan Afirka da dama da ke aikatau a ƙasar na cikin irin wannan hali

Asalin hoton, MURAT SENGUL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mata da yara 'yan Sierra Leone, waɗanda masu gidajen da suke yi wa aiki 'yan Lebanon suka kora sannan suka yi watsi da su bayan harin Isra'ila na neman mafaka a Beirut ranar Lahadi. 'Yan Afirka da dama da ke aikatau a ƙasar na cikin irin wannan hali
Bishiyoyi

Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA

Bayanan hoto, Yadda bishiyoyin Jacaranda suka yi haske kenan a birni mafi girma na Afirka ta Kudu, Johannesburg, ranar Alhamis.