Man Utd na son Branthwaite, Aston Villa za ta saye Rashford

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United a shirye take ta shiga farautar ɗanwasan baya na Everton da Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, a wannan bazara. (Sun - subscription required)

Aston Villa na da zaɓin tabbatar da mallakar ɗanwasan gaba Marcus Rashford, mai shekara 27 da ta karɓo aro daga Manchester United kan fam miliyan 40. (Teamtalk)

Liverpool na da tabbacin ɗanwasan gabanta na Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, da kuma ɗanwasan baya na Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 33, za su sabunta kwangilarsu kafin bazara. (Athletic - subscription required)

Manchester United na farautar ɗanwasan tsakiya na Borussia Dortmund da Jamus Felix Nmecha, mai shekara 24, wanda take son ɗaukowa kan fam miliyan 40. (Bild - in German)

Liverpool na ƙara matsi kan ɗanwasan tsakiya da take farauta daga RB Leipzig ɗan ƙasar Netherlands Xavi Simons, mai shekara 21, wanda za ta biya fam miliyan 67. (Caught Offside)

Ɗanwasan Bournemouth da Spain Dean Huijsen, mai shekara 19, shi ne na farko da Newcastle ke fatan ɗaukowa a wannan bazara. (Sun)

Bournemouth na son sayen golan Spain Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30 daga Chelsea yayin da kuma take da diba wani zaɓin na ɗauko Caoimhin Kelleher daga Liverpool. (Telegraph - subscription required)

Kocin Juventus Thiago Motta na fuskantar barazanar kora, inda kungiyar ke tattauna makomarsa. (Fabrizio Romano)

Arsenal da Liverpool da Chelsea na ribibin ɗanwasan baya na Ajax da Netherlands Jorrel Hato, mai shekara 19, amma kuma suna fuskantar hamayya daga Real Madrid. (Caught Offside)

Liverpool na da ƙarfin kashe sama da fam miliyan 100 domin ɗauko ɗanwasan gaba a wannan bazara yayin da ake tunanin ɗanwasanta na gaba ɗan ƙasar Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25 zai tafi. (Football Insider)