An kyale Van Dijk da Salah su koma Liverpool daga tawagar kasashensu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

'Yan wasan Liverpool Virgil van Dijk da Mohamed Salah za su koma atisaye ƙungiyar da wuri ba kamar yadda aka tsara sai an gama wasannin tawagar ƙasashensu ba.

An bai wa kyaftin ɗin Netherland Van Dijk jan kati a wasan da suka yi kunnen doki da Hungary a ranar Juma'a, an dakatar da shi daga buga wasan ranar Litinin na Nation League da za ta buga da Jamus.

Kyaftin ɗin Masar Salah ya ci kwallo a wasan neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afrika da suka yi nasara kan Mauritania da ci 2-0 a ranar Juma'a.

An yi tsammanin za ta buga wasan da za su yi a ranar Talata, sai dai kamar Van Dijk shi ma an kyale shi ya koma Liverpool gabanin lokaci.

Hakan jin daɗi ne ga kocin ƙungiyar Arne Slot, wanda zai fafata da Chelsea a Premier a ranar Lahadin 20 ga watan Oktoba.

Gabanin tafiya wasannin ƙasashe, Liverpool ce a saman teburi da maki ɗaya tsakaninta da gwarzuwar gasar Manchester City.