Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Sanda sun bai wa Bakayoko hakuri, bayan tsare shi
AC Milan ta sanar da cewar 'yan sanda sun nemi afuwa daga Tiemoue Bakayoko, bayan da suka tsayar da shi, suka bincike shi kan zargin harbe-harbe da bingiga.
Lamarin ya faru a Milan ranar 3 ga watan Yuli, inda aka yada faifan bidiyon da ya ja hankalin mutane da yawa a kafar sada zumunta ranar Litinin.
A faifan bidiyon an nuna dan wasan mai shekara 27, wanda ke buga wasannin aro a Milan daga Chelsea, wani dan Sanda na caje shi wasu biyu sun auna motarsa da bindiga.
Bayan da suka gama binciken dan kwallon tawagar Faransa daga nan suka sallameshi.
''Bayan harbe-harben da aka yi a inda dan wasan yake, 'yan sanda suka fara bincike,'' in ji mai magana da yawun AC Milan.
''An tsayar da dan wasan, amma jami'an tsaro na kammala binciken da suka gane ba hannunsa a laifin, sai suka bashi hakuri suka barshi ya tafi.''
BBC ta tuntubi dan wasan kan ko zai ce wani abin kan lamarin.
Bakayoko ya koma Milan kan yarjejeniyar kaka biyu a bara, wanda ya taka leda a San Siro a kakar 2018-19.
Ya buga wasa 18 a kakar da ta wuce da Milan ta lashe Serie A.
Dan kasar Faransa ya koma Chelsea daga Monaco a 2017 kan fam miliyan 40, wanda ya buga wa kungiyar Stamford Bridge wasa 43 a kakar farko.
Ya koma taka leda a Monaco a Agustan 2019 kan yarjejeniyar aro, daga nan ya koma taka leda aro a Napoli daga Oktoban 2020.