Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Neuer ya yi ritaya daga tsare ragar tawagar Jamus
Mai tsaron ragar tawagar Jamus, Manuel Neuer ya yi ritaya daga buga wa kasar tamaula.
Wanda ya lashe kofin duniya a 2014 ya buga wa kasar wasansa na karshe, bayan da Sifaniya ta yi nasara a kan Jamus a kwata fainals a Euro 2024.
Mai shekara 38 ya buga wa Jamus karawa 124, tun daga lokacin da ya fara yi mata tamaula a 2009 da buga mata manyan gasa takwas.
Neuer, wanda ya lashe kofin duniya a Brazil, an naɗa shi kyaftin din Jamus kafin gasar kofin duniya a Rasha a 2018, wanda Ilkay Gundogan ya karɓi mukamin a bara.
A makon nan Gundogan ya sanar da yin ritaya daga buga wa Jamus tamaula - tun farko Toni Kross ne ya rataye takalmansa, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2024.
Neuer zai ci gaba da tsare ragar Bayern Munich, wanda ya sabunta ƙwantiraginsa a ƙungiyar da zai kare a 2025.