'A kwai kuskure a rashin daukar Sancho a tawagar Ingila'

An wallafa

Tawagar 'yan wasan da Ingila ta sanar da hadawa a ranar Alhamis na da mahimmanci sosai domin kuwa ana sa ran ita ce za ta wakilce ta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.

'Yan wasa 28 din da sunayensu ya fito sune za su dauki hanyar zuwa Qatar, amma wadanda aka bari a kasa na da dan lokacin kalilan daga nan zuwa 13 ga watan Nuwamba da za a bayar da jarin sunayen karshe.

Daya daga cikin irin wadannan 'yan wasa shi ne dan wasan gefe na Manchester United Jadon Sancho, wanda kocin kasar Gareth Southgate ya gaza tafiya da shi, rabonsa da ya buka wasa tun watan Oktoban 2021.

"Akwai yan wasan da muke son tafiya da su idan lokaci ya yi," in ji Southgate a ranar Alhamis. "Amma hakan baya nufin wadanda muka kira sun samu wucewa kenan."

Sancho dai yana ta kokari ta yadda zai nuna Southgate ya yi kuskure wajen kin tafiya da shi, sa'o'i kadan bayan sanar da tawagar ya jefa kwallo guda a wasan da United ta yi a gasar Europa kan Sherrif Tiraspol.

"Babu dadi rashin kiran, amma zan ci gaba da aiki ba dare ba rana kuma ina fatan za a kira ni a nan gaba domin zuwa gasar cin kofin duniya," in ji dan shekara 22.

"Kawai zan kara mayar da hankali ne kan gobe na."

Sacho "ya fi cancanta sama da Grealish"

Da kwallon da Sancho ya ci wadda Erikson ya ba shi, Manchester United ta shiga gaban wasan.

A baya kokarinsa bai kai ya kawo ba a matsayin dan wasan da aka saya daga Dortmund a bara kan £73m, sai dai yanzu ya dauki sabon salon kokari karkashin koci Erik ten Hag.

Ya ci kwallo uku a wasanni shida da ya buga baya, wanda a wasa 24 da ya buga baya bai yi hakan ba.

"Na ji masa dadi sosai [Jadon]," in ji Ten Hag. "Na cin kwallo da ya sake yi, kuma dama tuni ya ci wasu a wasannin share fagen soma kakar wasanni. Komai nasa na tafiya daidai.

"Amma ina ganin sai ya sake kokari sosai, saboda ya iya kwallo sosai."

A matsayin da Sancho yake a yanzu ya zarce wasu daga cikin abokan kwallonsa da suke buga hannu guda da aka kira cikin tawagar Ingila.

Sau daya dan wasan gaban Arsenal Bukayo Saka ya ci kwallo a wannan kakar, yayin da dan wasan Manchester City Jack Grealish da na Chelsea Mason Mount har yanzu ba su jefa ko kwallo daya ba.

Tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes ya shaida wa BT Sport cewa: "Gareth yana daukar 'yan wasan da dalilinsa, watakila zai yi amfani da wadanda ya dauka a baya ne, amma a ganina ya fi Jack."