Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Modric zai mallaki hannun jari a Swansea City
Ɗan wasan tawagar Crotia mai taka leda a Real Madrid, Luka Modric zai sayi hannun jari a Swansea City.
Mai shekara 39 zai bi sawun waɗanda suka mallaki hannun jari a ƙungiyar da suka haɗa da Andy Coleman da Brett Cravatt da Nigel Morris da kuma Jason Cohen.
A watan Nuwambar 2024 aka saye hannun jari mafi tsoka a ƙungiyar daga Jason Levien da kuma Steve Kaplan.
Wannan shi ne karon farko da ake sa ran Modric zai mallaki hannu jari a wata ƙungiyar.
Ana kuma sa ran zai ci gaba da taka leda a Real Madrid, duk da cewar a karshen kakar nan yarjejeniyarsa za ta kare a Santiago Bernabeu.
Modric a lokacin da yake Tottenham ya fuskanci Swansea City tare da Joe Allen a 2012 - yanzu Allen yana Swansea a karo na biyu, shi kuwa Modric yana Real Madrid.
Modric zai sa hannun jari a Swansea mai buga Championship, wadda ta sanar da yin hasarar £15.2m, bayan cire haraji.