Eriksen ya amince zai koma Man United da taka leda

An wallafa

Dan kwallon tawagar Denmark, Christian Eriksen ya amince zai saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester United da taka leda.

Kwantiragin dan wasan mai shekar 30, ya kare a Brentford a kakar tamaula da aka kammala a watan jiya.

An fahimci cewar dan kwallon yana da damar ci gaba da taka leda a kungiyar da Thomas Frank ke jan ragama, amma ya zabi ya koma United.

An tanadi bai wa dan wasan yarjejeniyar kaka uku, amma sai an kammala auna koshin lafiyarsa a Old Trafford.

Eriksen ka iya zama na biyu da sabon koci, Erik ten Hag zai dauka a bana, bayan da kungiyar ke auna koshin lafiyar dan wasan Feyenoord, Tyrell Malacia a shirin komawa United da yake yi.

Eriksen ya koma buga Premier League, bayan da Brentford ta dauke shi a watan Janairu, bayan barin Inter Milan mai buga Serie A.

Ya bar buga gasar Serie A, bayan da aka dasa masa na'urar da ke taimaka masa yin nunfashi, hakan doka ne a babbar gasar Italiya, ba zai buga wasanni ba.

Dan kwallon ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake yi wa tawagar Denmark wasa a Euro 2020, gasar da Italiya ta lashe.

Tsohuwar kungiyar Eriksen, Tottenham wadda ya yi mata tamaula tsakanin 2013 zuwa 2020 ta so daukar dan wasan, amma ba ta mayar da hankali ba.