Salmai Albasu: Zabiyar da amonta ya karaɗe Arewa a shekarun da babu Tiktok
Salmai Albasu: Zabiyar da amonta ya karaɗe Arewa a shekarun da babu Tiktok
An wallafa
Ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa mata da suka yi fice cikin shekarun baya a arewacin Najeriya, Salmai Albasu ta ce tana alfahari da irin gudunmawar da ta bayar wajen wayar da kai don bunƙasa ilmi da yaƙi da fyaɗe.
Zabiyar ta yi fice tun daga shekarun 1970 wajen wayar da kai don jama'a su rungumi ilmi, su tura ƴaƴansu makaranta.