Man City ta ɗauki Reis daga Palmeiras

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta kammala ɗaukar matashin mai tsaron baya, Vitor Reis kan £29.6m daga Palmeiras ta Brazil.
Tuni ɗan wasan mai shekara 19 ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu da rabi.
Reis, ya yi karawa 22 a Palmeiras, wanda ya wakilci tawagar Brazil ta matasa ƴan kasa da shekara 17.
Palmeiras ta yi kokarin riƙe Reis zuwa karshen kakar nan, ko kuma ta bayar da aronsa, sai dai City ta dage sai dai ta biya ƙudinsa a watan nan na janairu.
Ɗan Brazil shi ne na biyu da City ta ɗauka a Janairun nan, bayan ɗan kasar Uzbekistan, Abdukodir Khusanov.
City mai riƙe da kofin Premier League na fama da ƴan wasa da yawa da ke jinya, hakan ya sa ƙungiyar ta fuskanci kalubale a kakar nan.
Haka kuma ƙungiyar Etihad na fatan sayen ɗaukar ɗan wasan Eintracht Frankfurt, Omar Marmoush kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo ta Janairu.








