Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fafaroma Francis ya bayar da haƙuri ga jama'ar Canada kan cin zarafi
A karon farko, Fafaroma Francis ya bayar da haƙuri a hukumance a ƙasar Canada kan batun irin cutarwar da makarantun katolika suka yi ga mazauna ƙasar a baya.
Ya bayar da haƙuri musamman kan irin rawar da cocin ta taka wurin sauya al'adun mutanen ƙasar wanda ya kira da mugun abu kuma mummunan kuskure.
Makarantun waɗanda akasarinsu cocin katolika ce ta kula da su, na da burin ilmantarwa da kuma sauya al'adu da tunanin yara waɗanda akasarinsu ke ƙauyukan Canada tun daga shekarun 1800 zuwa 1900.
Randy Ermineskin wanda yana daga cikin dattawa a yankunan da lamarin ya faru, ya gode wa Fafaroma Francis kan haƙurin da ya bayar.
"Ya fitar da sanarwa, Fafaroma ya ce a yi haƙuri. Wannan batun zai aika saƙo a fadin ƙasar nan a daidai lokacin da muke shiga siyasar duniya da wurare da Majalisar Dinkin Duniya, amma a yanzu sun ji da kunnensu. Duniya ta ji," in ji Randy.
Shi ma Desmond Bull wanda yana daga cikin masu faɗa a ji a al'ummomin da lamarin ya shafa, cewa ya yi:
"Ga wasu, wannan bayar da haƙurin ba shi ne abin da suke so ba domin su yafe. Ga wasu, wannan bayar da haƙurin ba wani abu bane. Duk ma dai yadda kuka ji, hakan ya yi daidai. Wani rahoto da kwamitin gaskiya da sasanci na Canada ya fitar a 2015 ya gano cewa an ci zarafin ɗalibai da dama kuma an yi watsi da su, kuma akwai kusan 300 daga cikinsu da ake zaton sun rasu.
Asalin mazauna ƙasar Canada dai sun sha fama da baƙin talauci a shekarun baya da kuma rashin lafiya.