Neymar ya gama buga tamaula a kakar bana

An wallafa

Dan wasan Paris St-Germain, Neymar ya gama buga wasan tamaula a bana, bayan da likitoci za su yi masa aiki a kafarsa a hagu.

Dan kwallon tawagar Brazil ya ji rauni a fafatawar da PSG ta doke Lille 4-3 ranar 19 ga watan Fabrairu.

Neymar na yawan fama raunin da yake dauke da shi a kafar hagunsa.

Bai buga wa Brazil wasa biyu ba a cikin rukuni a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, bayan da ya ji rauni a wasan farko da Serbia.

Tsohon dan wasan Barcelona, bai yi wa Brazil Copa America ba a 2019, bayan raunin da ya fama a kafarsa ta hagun.

A kakar 2021 ya yi jinya mai tsawo a sanadin kafar dai ta hadu.

Neymar ya ci kwallo 13 a Ligue 1 ya bayar da 10 an zura a raga a PSG a kakar nan.

Kungiyar da Christophe Galtier' ke jan ragama tana ta daya a teburin Ligue 1 da tazarar maki takwas, wadda ke kokarin daukar kofi na 11 jimilla.

Ranar Laraba, PSG za ta kara da Bayern Munich a wasa na biyu a Champions League zagayen 'yan 16 - Bayern ce ta je ta ci PSG 1-0 a wasan farko a Faransa.