Yadda mazauna Maiduguri suka rungumi kekuna bayan cire tallafin fetur

Yadda mazauna Maiduguri suka rungumi kekuna bayan cire tallafin fetur
An wallafa

Kafin watan Mayun 2023, hawa keke tamkar abin dariya ne a titunan birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabas - musamman ga magidanta.

Amma tun bayan ranar 29 ga watan na Mayu; lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a Najeriya, kekuna sun cika titunan birnin, wato babu talaka babu mai kuɗi.