Barcelona za ta dawo da Messi da Neymar, Arsenal na neman Gundogan

An wallafa

Barcelona na son sake sayen Lionel Messi, mai shekara 35 da kuma Neymar, mai shekara 31 daga Paris St-Germain . (Football Transfers)

Haka kuma mai bayar da shawara kan kwallon kafa na kungiyar ta PSG Luis Campos ya gana da wakilan Harry Kane a kan yuwuwar sayen kyaftin din na Ingila daga Tottenham. (Foot Mercato )

Real Madrid na son sayen Kylian Mbappe, daga PSG da dan bayan Bayern Munich Alphonso Davies, dan Canada mai shekara 22 da matashin dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham a bazaran nan. (Sky Sports)

Feyenoord za ta bai wa kociyanta Arne Slot dan Holland sabon kwantiragi domin hana shi tafiya Tottenham. (Mail)

Arsenal da Barcelona na sha'awar Ilkay Gundogan, wanda ke son Manchester City ta ba shi kwantiragin sama da shekara daya kafin ya ci gaba da zama a kungiyar. (Sport Bild)

Bayern Munich za ta sayar da Sadio Mane, a bazara kuma ana ganin da wuya ta yi amfani da zabin da take da shi na sayen dan bayan Portugal Joao Cancelo wanda ta karba aro daga Manchester City, ya zama dan wasanta na dindindin a kan fam miliyan 60. (Times)

Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Bayer Leverkusen da Arsenal a kan cinikin dan wasan tsakiya na Gunners Granit Xhaka, a kan kusan fam miliyan 13. (Standard)

Dan wasan gaba na Roma Tammy Abraham, dan Ingila ya ce dan bayan Chelsea da Ingila Reece James, ya gaya wa 'yan tsohuwar kungiyarsa cewa ya koma Stamford Bridge, inda kuma Manchester United da Newcastle United su ma suna sonshi. (Tuttomercatoweb,Standard)

Ana sa ran Brighton ta dauki dan wasan tsakiya na Jamus Mahmoud Dahoud, wanda kwantiraginsa zai kare da Borussia Dortmund a bazara. (Football Insider)

Dole ne Leeds United ta ci gaba da zama a gasar Premier, idan har tana son samun damar dawo da dan wasanta na tsakiya James Milner dan Ingila, ko da yake Brighton ce ke kan gaba wajen samun dan wasan idan kwantiraginsa da Liverpool ya kare a bazaran nan. (Mail)