Marciniak ne zai busa wasan Man City da Real Madrid

An wallafa

Hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta nada Szymon Marciniak a matakin wanda zai yi alkalancin wasan Manchester City da Real Madrid.

Ranar Laraba City za ta karbi bakunci Real a wasa na biyu a daf da karshe a Champions League.

Kungiyoyin biyun sun tashi 1-1 ranar 9 ga watan Mayu a Sifaniya, inda Vinicious Junior ya fara cin kwallo, Kevin de Bruyne ya farke wa City.

Wannan shine karo na shida da alkalin wasan dan kasar Poland zai busa fafatawar Real Madrid a gasar zakarun Turai.

Wasan karshe da ya busa wa Real shine wanda ta doke Chelsea a bara a zagaye na biyu a quarter finals da cin 3-2 a Santiago Bernabeu.

Ya fara da alkalancin da Real ta ci Roma 2-0 a Santiago Bernabeu a zagaye na biyu a zangon 'yan 16 a 2015/16 a Champions League.

Ya kuma busa karawar da Real Madrid da Borussia Dortmund suka yi 2-2 a fafatawar cikin rukuni a 2016/17.

Shine alkalin wasan da ya ja ragamar Real Madrid da Tottenham suka tashi 1-1 a Bernabeu a fafatawar cikin rukuni a kakar 2017/18.

Wasan da Real ta je ta ci Sheriff Tiraspol 3-0 a kakar 2021/22 a fafatawar rukuni, shine ya yi alkalanci.

Bayan Champions League, Marciniak shine ya busa karawar da Real Madrid da Atlético a wasan karshe a European Super Cup a 2018/19.