Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd da Arsenal na son daukar Dybala, Pogba da Di Maria za su sanya hannu kan koma wa Juve
Manchester United na neman hanyar kalubalantar Arsenal kan daukar dan wasa Paulo Dybala, bayan karewar kwantiraginsa da Juventus, yayin da ita ma Napoli ke nuna sha’awar daukar dan wasan na gaba mai shekara 28. (La Repubblica, via Star)
Dan wasan tsakiya na Portugal da Manchester City Bernardo Silva, mai shekara 27, ya shaida wa wakilinsa cewa yana son tafiya Barcelona a kakar wasan na. (Sport)
Fulham ta amince da sayen dan wasan tsakiya na Portugal, Joao Palhinha, mai shekara 26, kan £20m kuma shi ne dan wasan farko da suka amince su dauko a lokacin bazara. (Sky Sports)
Arsenal za su gana da Ajax a mako mai zuwa, a daidai lokacin da ake ci gaba da kokawar sayen mai tsaron baya na Argentina, Lisandro Martinez, yayin da ita ma Manchester United ke kokarin gwada sa’arta kan dan wasan mai shekara 24. (Athletic)
Barcelona ta amince da saida wa Manchester United dan wasan tsakiya na Netherland Frenkie de Jong, mai shekara 25, amma har yanzu ana ci gaba da sasantawa, kuma ba su kai ga tattaunawa kan batutuwa da dama ba. (Fabrizio Romano, Twitter)
A mako mai zuwa ne Juventus za ta rattaba hannu kan tafiyar dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 29, da na Argentina Angel di Maria, mai shekara 34, bayan sun bar Manchester United da Paris St-Germain. (Fabrizio Romano, Twitter)
Chelsea na samun ci gaba a kokarin dauko mai tsaron gid ana Netherland Matthijs de Ligt, mai shekara 22, bayan Juventus ta sassauto kan farashin dan wasan. (CBS Sports, Twitter)
Leeds United da AC Milan, na tuntuba kan dan wasan tsakiya na Ivory Coast, Hamed Traore, mai shekara 22. (Corriere dello Sport, via Yorkshire Evening Post)
Leeds ma ta fara tattaunawa kan farashin fam miliyan 12, domin dauko dan wasan tsakiya na Amirka da RB Leipzig Tyler Adams, mai shekara 23. (Mail)
Crystal Palace na son daukar Dwight McNeil daga Burnley ya yin da West Ham kuma ken una sha’awar dan wasan Ingilar, mai shekara 22, said ai kuma ta yiwu Burnley ta bukaci sama da fam miliyan 10 kan dan wasan. (Sun)