'Ko Barcelona za ta huce a kan Valencia a La Liga?

Asalin hoton, Getty Images
Valencia za ta karbi bakuncin Barcelona, domin buga wasa mako na 12 a gasar La Liga da za su kara ranar Asabar.
Barcelona mai maki 28 tana ta biyu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana, Valencia mai maki 15 tana ta tara a teburin.
Real Madrid ce ta daya mai maki 31 da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona, bayan wasa 11 da kowacce ta buga a kakar nan.
Wasa uku Valencia ta yi nasara a kan Barcelona daga 30 baya da suka kara.
A shekarar 2020 Valencia ta ci Barca 2-0 a gidanta, shi ne na farko da ta yi nasara tun 2007 a kan kungiyar Nou Camp.
Sauran wasa biyun da Valencia ta yi nasara a Nou Camp ne, wadda ta ci 3-2 a 2014 da kuma 2-1 a 2016.
To sai dai a wasa tara kusa-kusa nan Valencia ta yi nasara a hudu har da doke Barcelona 2-1 a 2019 ta lashe Copa del Rey.
Tuni dai aka yi waje da Barcelona daga gasar Champions League ta bana, za ta koma buga Europa League karo na biyu a jere.
Bayern Munich ce ta ci kungiyar Nou Camp gida da waje kamar yadda ta yi mata a bara.
Bayern ce ta ja ragamar rukuni na uku a gasar Zakarun Turai, sai Inter Milan ta biyu, sannan Barcelona ta uku da kuma Victoria Polzen mara maki ko daya.
Wasan da Valencia da Barcelona suka kara a bara:
2021/2022
Spanish La Liga Su 20Feb 2022
- Valencia 1 - 4 Barcelona
Spanish La Liga Su 17Oct 2021
- Barcelona. 3 - 1. Valencia
Tuni kociyan Barcelona ya bayyana 'yan wasa 21 da ya je da su Valencia domin buga fafatawar.
'Yan kwallon Barcelona:
Ter Stegen, Bellerín, Piqué, Sergio, Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Marcos Alonso da Jordi Alba.
Sauran sun hada da Kessie, De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Iñaki Peña, Balde, Gavi, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.
Wasannin da za a buga ranar Asabar:
- UD Almeria da Celta de Vigo
- Cadiz da Atletico de Madrid
- Sevilla da Rayo Vallecano
- Valencia da FC Barcelona
Ranar Lahadi Real Madrid za ta karbi bakuncin Girona a wasan mako na 12 a gasar ta La Liga.









