Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Ana yin tir da tuban Bello Turji, an dakatar da ɗaukar sabbin 'yan sanda aiki
Kamar kowane ƙarshen mako, wannan ma mun duba muhimman abubuwan da suka faru a sassan Najeriya.
Al'ummar Najeriya na ci gaba da Allah-wadai tun bayan fitowar wasu bayanai kan fitaccen ɗan bindigar nan Bello Turji Kachalla da ake cewa ya rungumi sulhu bayan tabbatar da tubansa.
A ranar Lahadi ne gwamanatin Zamfara ta fitar da wata sanarwa da ke cewa fitaccen ɗan bindigar ya tuba, kuma ya rungumi zaman lafiya bayan ya shafe shekaru yana satar mutane da kashe na kashewa.
Sai dai wannan labari ya zo wa galibin 'yan kasar da ke tantama da mamaki, inda galibin mutane har a shafukan sada zumunta ke tafka muhawara da nuna shakku kan tuban Bello Turji.
Mataimakin gwamanan Jihar ta Zamfara ne ya gabatar da sanarwar game da mutumin da yawancin mutane a arewacin Najeriya ke kira 'Sarkin 'yan Ta'adda.
An shafe shekaru jami'an 'yan sanda na nemansa ruwa-a-jallo domin laifukan ta'addancin da ake tuhumarsa da aikatawa a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina masu makwabtaka.
An dakatar da ɗaukar sabbin ƴan sanda aiki
Hukumar da ke kula da batutuwan da suka shafi aikin dan sanda a Najeriya (PSC) ta dakatar da aikin daukar sababbin kuratan ƴan sanda.
Hukumar ta dauki wannan matakin ne kasa da sa'a 24 bayan da sufeto-janar na ƴan sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana bacin ransa kan wani talla da aka wallafa kan daukan masu sha'awar aikin dan sandan.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar, sufeto-janar din ya bukaci ƴan Najeriya su yi watsi da tallan da aka wallafa a wsu manyan jaridun kasar.
A nata bangaren, hukumar ta PSC ta ce akwai wani rashin fahimta tsakaninta da rundunar ƴan sandan Najeriya.
Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya ce nan ba da dadewa ba za a sasanta kan wannan batun. Ya kuma ba masu sha'awar aikin da su jinkirta zuwa wani lokaci nan gaba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta PSC ta taba kai karar rundunar ƴan sandan Najeriyar da tsoho sufeto-janar Mohammed Adamu kan gudanar da aikin daukan kuratan ƴan sanda 10,000 a 2019, sai dai daga baya sun sasanta.
Amurka za ta mayar wa Najeriya dala miliyan 23 da ake zargi Abacha ya sace
Amurka ta amince ta mayar da karin dala miliyan 23 ga Najeriya.
Kudaden dai wani bangare na kudaden da ake zargi tsohon shugaban mulkin sojan kasar Sani Abacha ya sata.
A ranar Talatar da ta wuce ne kasashen biyu suka cimma yarjejeniya a Abuja kan batun kudin.
Ministan Shari'a na Najeriya, Abubakar Malami, ne ya sanya hannu a yarjejeniya, yayin da jakadar Amurka a kasar Maru Leonard, ta wakilci kasarta a yarjejeniyar.
Malami ya ce idan an dawo da kudin za a kashe su ne wajen ayyukan gina kasa.
A 2020, Amurka ta dawo wa Najeriya da fiye da dala miliyan 300.
Ana zargin tsohon shugaban kasar Abacha, da ya rasu a 1998, da sace biliyoyin dalolin kasar tare da ajiye su a kasashen waje.
Kazalika a shekarun baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta dawo da wasu kudaden da aka sace aka boye su a kasashe kamar Switzerland da Burtaniya da kuma Amurka.
Najeriya ta sakar wa kamfanonin sufurin jiragen sama na waje kuɗinsu da ta riƙe
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa kamfanonin sufurin jirgin sama na ƙasashen waje kuɗinsu dala miliyan 265 bayan shafe watanni ba sa iya fitar da kuɗin zuwa gida.
Bayanan kuɗin da aka saki ranar Juma'a sun nuna cewa an ba da dala miliyan 230 a matsayin tallafi na kuɗin ƙasar waje, yayin da aka ba da miliyan 35 a wani matsayin daban.
Shugaban sashen hulɗa da jama'a na CBN, Osita Nwanisobi, ya ce Gwamnan CBN Godwin Emefiele da tawagarsa sun damu da halin da ake ciki da kuma halin da ɓangaren sufurin jiragen sama zai shiga a Najeriya.
Nwanisobi ya ƙara da cewa CBN ba ya adawa da kowane kamfani da ke son kwashe kuɗinsa daga Najeriya zuwa ƙasarsa ta asali, yana mai cewa "bankin ya dage ne kan bin doka wajen kwashe kuɗin".
Sakin kuɗin zai sanyaya zuciyar kamfanonin yayin da tuni wasu daga cikinsu suka rage shiga Najeriya kan hakan, wasu kuma suna shirin daina zuwa baki ɗaya.
Kuɗaɗen na sayen tikiti ne da 'yan Najeriya da sauran matafiya ke saya da kuɗin naira, inda shi kuma CBN yake bai wa kamfanonin adadin kuɗin a dalar Amurka.
Rushewar gini a Abuja ta kashe mutum biyu
Rashewar da wani gini mai hawa biyu a Abuja a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya yi ta kashe mutum biyu tare da jikkata wasu.
Jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, NEMA na ci gaba da gudanar da aikin ceto.
A cewar rundunar tsaron 'yan ƙasa ta Civil Defense, ginin ya rufta ne da tsakar dare ranar Alhamis - washegarin Juma'a - a kan titin Hamza Abdullahi da ke yankin Kubwa.
Wani mazaunin unguwar ya ce an ceto wasu mutane da suka jikkata, inda kuma aka wuce da su zuwa asibiti.
Bayan faruwar lamarin, Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kai ziyara wurin, inda ya bukaci a gudanar da bincike kan dogayen gine-ginen da ke unguwar domin sanin kwarinsu.
Kungiyar Izala ta aurar da mata marayu 20 a Abuja
Ranar Laraba Kungiyar Izalatul Bidi'a wa Iqamatus Sunnah reshen babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ta gudanar da auren 'yan mata marayu 20.
Kwamitin kungiyar na babban birnin shi ne ya shirya bikin daurin auren a karkashin inuwar kungiyar ta kasa.
Bayan daura auren an bai wa ma'auratan kayan daki da jari na tsabar kudi domin yin sana'a.
Ga hotunan yadda bikin ya wakana daga masallacin Berger da ke Unguwar Utako ranar 24 ga watan Agustan 2022.
An sako malaman coci mata da aka sace a Jihar Imo
An sako malaman cocin nan mata hudu da 'yan bindiga suka sace a jihar Imo da ke kudancin Najeriya.
An sace malaman ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen ibada a ranar 21 ga watan Augusta.
Ma'aikatan da aka sako sune Johannes Nwodo da Christabel Echemazu da Liberata Mbamalu da kuma Benita Agu.
Cikin wata sanarwa da wata kungiyar kiristoci mata mai suna The Sisters of Jesus the Savior, ta fitar ta ce bayan shafe kwanaki biyu ana addu'oi game da sace matan, a yanzu an sako su kuma suna cikin koshin lafiya.
Batun sace kiristoci a Najeriya ya zamo ruwan dare gama duniya a shekarun baya-bayan nan, matsalar da shugabannin kiristocin a matakai da dama ke nuna damuwa a kai tare da jan hankalin gwamnati da ta kara ba wa bangaren tsaro muhimmancin da ya dace don kare al'ummarta.
A lokuta da dama masu satar mutane kan sace malaman coci sannan su nemi kudin fansa.
Matsalar tsaro a Najeriya dai na kara kamari duk da kokarin da gwamnatin tarayya ta ce tana yi wajen kawo karshen matsalar.