Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guardiola zai bar City a bazarar baɗi, United na nazarin Frank da Pochettino
Ana tunanin kocin Manchester City Pep Guardiola zai kawo ƙarshen zamansa a ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar wasan mai zuwa. (Mail)
Manchester United ta tattauna da wakilan kocin Brentford Thomas Frank da kuma tsohon kociyan Chelsea Mauricio Pochettino, yayin da ake tunanin za ta iya korar Erik ten Hag. (Telegraph)
Al-Ittihad na zawarcin mai tsaron ragar Manchester City Ederson kuma ƙungiyar ta Saudi Pro League na iya miƙa tayin farko na fam miliyan 25 kan ɗan wasan na Brazil mai shekaru 30. (Mail)
Tsohon kocin Brighton Roberto de Zerbi shi ne na huɗu a jerin sunayen da Chelsea ke nazari a neman sabon koci, yayin da Thomas Frank na Brentford da Enzo Maresca na Leicester City da kuma Kieran McKenna na Ipswich Town ke gabansa. (Mail)
Kocin Leicester City Enzo Maresca ya ƙi amincewa da tayin Sevilla inda ya ke son ya ci gaba da zama a gasar Premier, kuma yana jiran shawarar da Chelsea za ta yanke bayan tattaunawa da ƙungiyar ta Stamford Bridge. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan tsakiya na Morocco Sofyan Amrabat, mai shekara 27, ya ce zai tattauna da Manchester United game da makomarsa, inda kulob ɗin na Old Trafford ke da zaɓin mayar da zaman aronsa daga Fiorentina zuwa na dindindin. (Ziggo Sport)
Jerin sunayen da Burnley ta fitar na wanda zai maye gurbin kocinta Vincent Kompany, wanda ke daf da komawa Bayern Munich, ya haɗa da tsohon kocin Chelsea Frank Lampard da tsohon kocin Nottingham Forest Steve Cooper. (Patreon)
Zakarun Jamus Bayer Leverkusen na daf da sayen ɗan wasan tsakiyar Sifaniya Aleix Garcia, mai shekara 26, daga Girona kan farashin kusan Yuro miliyan 15-20 (£11.8m- £15.7m). (Sky Sports Germany)
Ana sa ran ɗan wasan Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, zai bar Tottenham domin samun damar buga wasa akan kari. (Football Insider)
Manchester United na shirin jira har sai bayan an rufe kasuwar musayar ƴan wasa ta bazara kafin ta inganta kwantiragin ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19. (Telegraph)