Girke-girken Ramadan: Yadda ake haɗa miyar Beef Bulgogi

Bayanan bidiyo, Girke-girken Ramadan
Girke-girken Ramadan: Yadda ake haɗa miyar Beef Bulgogi
An wallafa

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda ake haɗa miyar beef bulgogi.

Maryam Tafida wadda aka fi sani da tafeeda'sglamour ko kuma cookwithtafidah gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake wannan ƙayatacciyar miya ta beef bulgogi mai matuƙar burgewa.