Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amorim na fatan Man United za ta lashe Europa League na bana
Ruben Amorim na fatan Manchester United za ta yi abin kirki a kan West Ham ranar Lahadi a Premier kafin wasan karshe a Europa League da Tottenham.
United za ta karɓi bakuncin West Ham United a wasan mako na 36 a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
West Ham ce ta doke United 2-1 a wasan farko ranar 27 ga watan Oktoban 2024, kuma West Ham na fatan nasara gida da waje a kan United a karon farko tun 2006/07.
To sai dai West Ham ta kasa yin nasara a kan United a wasa 16 baya, wadda aka doke karo 13 da canjaras uku.
Bayan da ƙungiyar Old Trafford ta yi waje da Athletic Bilbao a wasan daf da karshe a Europa League, yanzu za ta kece raini da Tottenham a cikin watan nan a karawar karshe.
Wannan ce damar da ta rage ga Manchester United, domin zuwa Champions League a baɗi da zarar ta yi nasara a kan Tottenham.
United tana mataki na 15 a kasan teburin Premier League da maki 39 da tazarar maki ɗaya tsakani da Tottenham ta 16.
Amorim ya ce a karawa da West Ham zai yi taka tsantsan wajen ƴan wasan da zai zaɓo, domin kada a samu matsala daga masu koshin lafiya.
Ƴan wasan da Amorin ke cewa ba zai yi kasada ba, sun haɗa da Harry Maguire da Noussair Mazraoui.
Sauran har da Matthijs de Ligt da Lisandro Martinez da Diogo Dalot, yayin da Joshua Zirkzee ke jinya.
Da zarar United ta kammala wasan West Ham a Premier ranar Lahadi daga nan za ta je Chelsea a Stamford Bridge a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Za a buga wasan karshe a Europa League tsakanin Tottenham da Manchester United ranar Larabar 21 ga watan Mayu.
Daga nan kuma United ta karkare da karɓar bakuncin Aston Villa a wasan makon karshe na 38 ranar 25 ga watan Mayu, daga shi a rufe labulen Premier League na bana.