Real Madrid za ta san wadda za ta haɗu da ita a Copa del Rey ranar Litinin

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta san ƙungiyar da za ta kara da ita a Copa del Rey na bana a jadawalin da za a yi ranar Litinin a hedikwatar hukumar ƙwallon kafar Sifaniya.
Za a buga wasan zagaye ɗaya ba kamar yadda aka saba na al'ada ba da ake yi gida da waje, inda aka ware ranar 5 ko 6 ga watan Janairun 2025 a wasannin farko.
Bayan da Real Madrid ba ta buga karawa biyu ba, yanzu tana tukunyar farko da ta ƙunshi ƙungiyoyin da za su kara a Spanish Super Cup da ya haɗa har da Athletic Club da Barcelona da kuma Mallorca.
Za a raba jadawalin da Real Madrid take da waɗanda ke tukunya ta biyar su huɗu daga gasar Sifaniya mai daraja ta huɗu da ya haɗa da Barbastro da Pontevedra da UD Logronés da kuma Deportiva Minera, waɗanda su kai zagayen ƴan 32.
Waɗanda za su buga gurbin zagaye na ƙungiyoyi 32:
Tukunyar farko (Waɗanda za su kara a Super Cup a bana): Real Madrid, Barcelona, Athletic Club da kuma Mallorca.
Tukunya ta biyu (Masu buga La Liga): Real Valladolid, Celta de Vigo, Las Palmas, Rayo Vallecano, Betis, Valencia, Leganés, Atlético, Osasuna, Getafe, Sevilla da kuma Real Sociedad.
Tukunya ta uku (Masu buga gasar Sifaniya mai daraja ta biyu): Elche, Granada, Huesca, Eldense, Almería, Racing de Santander, Tenerife, Racing de Ferrol da kuma Cartagena.
Tukunya ta huɗu (Masu buga gasa mai daraja ta uku a Sifaniya): Ourense CF, Marbella da kuma Ponferradina.
Tukunya ta biyar (Masu buga gasa mai daraja ta huɗu a Sifaniya): Barbastro, Pontevedra, UD Logroñés da kuma Deportiva Minera.











