Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu uku da zan yi kan matsalar tsaro a Katsina - Dikko Radda
Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina a jam'iyyar APC mai mulkin jihar, Dikko Umar Radda, ya ce akwai abu uku da zai saka a gaba wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar.
Ɗan takarar ya bayyana hakan cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa da muke kawo muku da 'yan takarar muƙamai daban-daban yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023 a Najeriya.
Katsina na cikin jihohin arewa maso yammacin ƙasar da suka fi fuskantar hare-haren 'yan fashin daji da ke kashe mutane tare da ƙona gidajensu da gonaki haka kawai.
A watan Mayu mai zuwa Gwamna Aminu Bello Masari na APC zai kammala wa'adi na biyu a matsayin gwamna, inda babbar jam'iyyar adawa ta PDP da sauransu za su nemi ƙwace mulkin jihar.