Amorim na son Bruno Fernandes ya ci gaba da taka leda a Man United

Asalin hoton, PA Media
Kocin Manchester United Ruben Amorim na son kyaftin ɗin kulob ɗin Bruno Fernandes ya ci gaba da taka masa leda duk da sha'awar da ƙungiyoyin Saudiyya ke nunawa a kansa.
Kwantaragin Fernandes zai ƙare a 2027 amma an sha alaƙanta ɗan ƙasar Portugal ɗin da ƙungiyar Al-Hilal da aka ce za ta ba shi gagarumin albashi idan ya koma kafin fara gasar Kofin Duniya ta ƙungiyoyi a wata mai zuwa.
Amorim na sane da cewa dole ne ya sayar da wasu 'yanwasa kafin ya iya ƙarfafa tawagar tasa a kaka mai zuwa.
Wannan matsala za ta fi ƙamari idan United ɗin ta gaza lashe gasar Europa League domin samun gurbin gasar Champions League ta baɗi.
"Tunaninmu bai sauya ba," a cewarsa. "So muke mu riƙe mafi ƙwarewa a 'yanwasanmu - kuma a bayyane take Bruno yana cikin manyan 'yanwasa a duniya. Muna son ya ci gaba da zama a nan."
Fernandes ya ci ƙwallo 19 tare da taimakawa wajen cin wasu 18 a kakar nan.
"Amfaninsa a fili yake - ba kawai saboda yawan cin ƙwallo ba har ma da yadda yake murza leda da kuma tasirin da yake da shi cikin shekara biyar a nan," in ji Amorim.
"Ba abin damuwa ba ne idan ƙungiyoyi da yawa na neman ɗanwasa kamar Bruno. Shugaba ne kuma shi ne kyaftin, saboda haka yana da amfani sosai."










