Sifaniya ta lallasa Switzerland a gasar cin kofin duniya

An wallafa

Sifaniya ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta mata a karon farko bayan da ta nuna bajintarta inda ta doke Switzerland da ci 5-1.

A cikin makon da ya gabata ne Japan ta doke Sifaniya da ci 4-0 a wasansu na karshe na rukuni a Wellington.

To sai dai 'yan wasan Sifaniyan sun dawo cikin salo inda suka zura kwallaye hudu a mintuna 45 na farkon wasan a gaban 'yan kallo 43,217 a filin wasan Eden park da ke kasar Newzealand.

Tawagar Sifaniya ita ce ta farko da ta kai matakin dab da kusa da na ƙarshe, za kuma ta kara da kasar da ta yi nasara a wasan da za a yi ranar Lahadi tsakanin Netherlands da Afirka ta Kudu a Wellington ranar Juma'a mai zuwa.

A daya wasan zagaye na biyu da aka buga Japan ta doke Norway da ci 3-1 don tsallakawa zuwa wasan daf da na kusa da na karshe.

Yanzu za ta kara da kasar da ta yi nasara a wasan da za a buga tsakanin Amurka da Sweden a zagaye na gaba.