Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Mahmud Gwammaja

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Mahmud Gwammaja
An wallafa

A wannan makon, filin Ku San Malamanku ya karɓi baƙuncin Sheikh Muhammad Mahmud Mustapha Gwammaja.

An haife shi ranar 3 ga watan Fabrairun 1985 a unguwar Gwammaja da ke ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano.

Shehin malamin ɗa ne ga Malam Mudi Madabo, kuma ya haddace Ƙur'ani a makarantar Gwani Dan Zarga da ke unguwar Koki.