Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin da ake ciki a Kuriga bayan sace 'yan makaranta 287
Halin da ake ciki a Kuriga bayan sace 'yan makaranta 287
An wallafa
A ranar 7 ga watan Maris ne dai aka sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu a garin da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
A yanzu haka al'ummar garin na Kuriga na ci gaba da zaman dar-dar tun bayan sace 'yan makarantar su fiye da 280.
BBC ta aike da tawaga ta musamman zuwa garin na Kuriga domin ganin halin da al'ummar garin ke ciki tun bayan faruwar al'amarin mai ban takaici.
Ga kuma rahoton da wakilin BBC, Chris Ewokor ya hada mana.