Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barca na shirin sayen Diaz, ƙungiyoyin firimiya na bibiyar Omorodion
Barcelona ta nuna sha’awar sayen ɗan wasan gaban Liverpool da Colombia mai shekara 27, Luis Diaz. (Sport - in Spanish)
Wolves na shirin ɗaukar kodai mai tsaron gidan Arsenal mai shekara 25, Aaron Ramsdale, ko na Liverpool mai shekara 25, ɗan ƙasar Ireland, Caoimhin Kelleher, ko kuma mai tsaron gidan Sunderland, ɗan shekara 23, Anthony Patterson domin mayen gurbin Jose Sa, ɗan ƙasar Portugal mai shekara 31 wanda zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana. (Sun)
Manchester City za ta saurarin tayin ɗan wasan tsakiyar ta, kuma ɗan Ingila mai shekara 28, Jack Grealish a bana. (Football Insider)
Ita ma Barcelona za ta yi nazari a kan tayin ɗan wasan bayan ta, kuma ɗan Uruguay mai shekara 25, Ronald Araujo a bana, kuma Manchester United tana cikin masu bibiyar ɗan wasan. (Sport - in Spanish, via Goal)
Crystal Palace za ta shiga zawarcin ɗan wasan tsakiyar Club Bruges ɗan Najeriya mai shekara 23, Raphael Onyedika. (Sun)
Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United sun shiga takarar sayen ɗan wasan bayan Real Madrid da Faransa, ɗan shekara 28, Ferland Mendy. (L'Equipe - in French)
Borussia Dortmund za ta biya £35m domin sayen ɗan wasan bayan Chelsea mai shekara 22, wanda yanzu haka ke taka mata leda a matsayin ɗan wasan aro, Ian Maatsen . (Mirror)
Wasu ƙungiyoyin gasar Firimiya na bibiyar ɗan wasan gaban Atletico Madrid mai shekara 19, kuma ɗan Sifaniya, Samu Omorodion, wanda ke zaman aro a Alaves. (AS - in Spanish)
Manchester City na fuskantar ƙalubale daga Arsenal da Liverpool, a ƙoƙarin ta na sayen ɗan wasan bayan Wolves kuma ɗan Algeria mai shekara 22, Rayan Ait-Nouri. (Mirror)
Manchester United da Newcastle na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 29, Adrien Rabiot idan bai sabinta kwangilar sa da Juventus ba. (Calciomercato - in Italian)