An ci tarar Real Madrid saboda kalamn cin zarafin Guardiola

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta ci tarar Real Madrid, saboda kalaman cin mutunci da magoya bayanta suka yi wa Pep Guardiola.

Haka kuma an bukaci ƙungiyar ta Sifaniya ta biya tarar Yuro 30,000 kimanin (£24,800).

An kuma ce Real za ta rufe wani sashe na filinta a wasan da za ta yi a gasar zakarun Turai a Santiago Bernabeu.

Sai dai wannan hukuncin sai nan da kaka biyu ake sa ran Real za ta gudanar da shi.

An yi wa kociyan Sifaniya kalaman ne a wasan da Real ta yi nasara 3-1 a kan City da Guardiola ke jan ragama a Champions League a farkon watan Fabrairu a Bernabeu.

Nasarar da Real ta yi ya sa ta kai zagayen ƴan 16 da cin 6-3 gida da waje, wadda za ta fuskanci Atletico Madrid a zagayen gaba.

Real Madrid mai rike La Liga na bara, ita ce mai Champions League, kuma na 15 jimilla.