El Clasico: Me ya sa karawar Madrid da Barca za ta fi zafi a bana?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A kodayaushe wasan El-Clasico, fafatawa ce mai jan hankali tsakanin magoya bayan ƙwallon ƙafa a faɗin duniya, to amma babban abin da zai ja hankali a karawar hamayyar wannan Asabar ɗin tsakanin manyan giwayen Sifaniya, Real Madrid da Barcelona, shi ne kamo tarihi da Real Madrid ke fatan yi.

Nasara ko canjaras guda tawagar Carlo Ancelotti ke buƙata a fafatawar yau, domin kamo tarhinin Barcelona na wasa 43 ba tare da an doke ta ba a La Liga.

Zakarun na Sifaniya sun buga wasa 42 a jere a gasar La Liga ba tare da doke su ba.

To sai dai wasan ƙungiyar na 43 a gasar, karawa ce da babbar abokiyar hamayyarta a gasar wato Barcelona, wadda a yanzu ke riƙe da tarihin bajintar wasa 43 ba tare da an doke ta ba a La Liga, da ta kafa tsakanin 2017 da 2018.

Yaushe bajintar ta faro?

Rabon da a doke Real Madrid a La Liga tun ranar 24 ga watan Satumban 2023, lokacin da Atletico Madrid ta yi nasara a kanta da ci 3-1.

Tun daga lokacin ta yi nasara sau 31, da canjaras 11, sannan babu ƙungiyar da ta doke ta a gasar.

Hakan ya ba su damar ɗaukar kofin gasar La Liga a kakar wasan da ta gabata, inda suka ɗauka da tazarar mako 10, sannan babu wanda ya doke kungiyar a gasar Zakarun Turai ta Champios League, inda a ƙarshe suka ɗauki kofin bayan doke Borussia Dortmund a wasan ƙarshe.

Dangane da ‘yan wasan da suka fi yi wa ƙungiyar bajinta, Federico Valverde ya taka muhimmiyar rawa ga ƙungiyar, wanda ya buga duka waɗanann wasanni da ƙungiyar ta yi ba tare da an doketa ba, in ban da guda ɗaya.

Haka kuma, tun bayan rashin nasarar Atletico, babu wanda ya ci wa Madrid ƙwallaye a gasar La Liga masu yawa, kamar Vinicius Junior da ya ci 19.

Dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham shi ne na gaba wanda ya zura kwallaye 14.

Yaya ƙoƙarin Real Madrid, idan an kwatanta da Barcelona?

Barcelona na buƙatar doke Real Madrid a wasan na yau Asabar don ci gaba da riƙe kambinta.

Barca – wadda ke jan ragamar La Liga a bana – ta fara kafa tarin nata ne a watan Afrilun 2017 lokacin da ta doke Real Sociedad 3 -2, sannan ya ƙare a watan Mayun 2018 lokacin da ta yi rashin nasara a hannun Lenavte da ci 5-4, lokacin da wasa biyu ne kawai ya rage mata ta ƙare kakar ba tare da an doketa ba.

Idan aka kwatanta ƙungiyoyin biyu, Tawagar Barcelona ta shekara shida da suka wuce, tawagar ce mai ƙarfi da zaƙa-ƙuran ‘yan wasa.

Dan wasan gaban Barca Lionel Messi ya taka rawar gani a wasannin 43 da ƙungiyar ta yi a jere ba tare da an doke ta ba, inda ya zura kwallo 58 a raga, fiye da ƙwallo 48 da Vinicius da Bellingham suka zura a wasa 42 jimilla tsakaninsu, da ƙungiyar ta yi ba tare da an doke ta ba.

Barcelona kuma ta ci wasa 34, tare da canjaras tara, saɓin Madrid wadda ta ci wasa 31 tare da canjaras 11, kodayake Barca ta fi yawan wasanni.

A ɓangaren tsaron gida, Real Madrid ta fi bajinta, inda ta yi wasa 23 ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba, saɓanin Barcelona mai wasa 19, sannan ƙwallo 27 aka zura wa Madrid a tsawon lokacin, ba kamar Barcelona da aka zura wa 33 ba a tsawon bajintar tata.

Haka kuma Madrid ya cimma wannan matsayi ne ƙarƙashin koci guda, Carlo Ancelotti, saɓanin Barca da ta cimma bajintar ƙarƙashin koci biyu, Luis Enrique da Ernesto Valverde.

Bajintar yawan wasa ba tare da doke ƙungiya ba a Turai

Ƙungiyar da ta fi yawan wasa da tare da an doketa ba a nahiyar Turai ita ce Bayern Munich wadda ta taɓa buga wasa 53 a jere ba tare da an doketa ba.

Daga nan sai Arsenal, da ta taɓa buga wasa 49 ba tare da rashin nasara ba.