Wasa biyar kenan a jere Man United ba ta ci Tottenham ba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A daren jiya Alhamis ne Manchester United ta sha kashi a filin wasa na Tottenham Hotspur a zagayen kwata fayinal na gasar Carabao Cup.

Hakan ya bai wa Tottenham damar samun gurbin karawa da Liverpool mai raiƙe da kofin gasar a zagayen semi fayinal.

Solanke ne ya fara zira ƙwallo a ragar Man United minti 15 da take wasan, kafin Kulosevski ya ci ta biyu minti ɗaya da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai a minti na 63 Zirkzee ya zare wa United ɗaya, sannan Amad Diallo ya farke ta biyun a minti na 70.

Sai dai Solanke ya ƙara ta uku, yayin da kyaftin Son ya ci ta huɗun daga bugun kwana saura minti biyu kafin cikar lokaci. Bayan cikar lokacin da minti huɗu Evans ya ci wa United ta ukun.

Sakamakon na jiya na nufin Tottenham ba ta yi rashin nasara ba a hannun Man United cikin wasa biyar da suka buga a jere a dukkan gasanni, inda ta ci uku kuma suka yi canjaras a biyu.

Rabon da Man United ta doke Tottenham tun a wasan Premier League na ranar 19 ga watan Oktoban 2022, inda ta doke ta 2-0.

Kazalika, Arsenal kuma za ta fuskanci Newcastle a zagayen na semi fayinal.

Liverpool da ke jagorantar teburin gasar Premier ta lashe kofin har sau 10 mafiya yawa a tarihi, za kuma ta kara da Spurs ne zagayen farko a Tottenham Hotspur Stadium kafin a buga na biyun a Anfield.

Arsenal kuwa za ta kara da Newcastle a filin wasa na Emirates Stadium a wasan farko, sannan a buga na biyun a St James' Park.

Haɗin ka iya haifar da wasan hamayyar birnin Landan a wasan ƙarshe na gasar, kodayake dai Arsenal da Tottenham ba su taɓa haɗuwa a wasan ƙarshe na wata babbar gasa ba.

Amma sun haɗi a zagayen semi fayinal na League Cup sau huɗu - 1968, 1987, 2007 and 2008.

Wasannin semi fayinal ɗin za a buga su ne a makon 6 ga watan Janairun 2025, sai kuma a buga zagaye na biyu a makon 3 ga watan Fabrairu.

Filin wasa na Wembley ne zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe ranar 16 ga watan Maris.