Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid za ta yi wasan karshe a La Liga da Athletic Club
Ranar Lahadi 4 ga watan Yuni za a kammala wasannin La Liga na kakar bana, inda za a yi karawa 10 duk a lokaci daya.
Cikin wasannin da za a yi har da wanda Real Madrid za ta karbi bakuncin Athltic Bilbao a Santiago Bernabeu.
Real Madrid tana mataki na biyu a kan teburin La Liga da maki 77, ita kuwa Bilbao mai maki 50 itace ta takwas a teburin.
Kungiyoyin biyu sun fara fuskantar juna a gasar ranar 22 ga watan Janairun 2023, inda Real Madrid ta ci 2-0.
Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Karim Benzema da kuma Toni Kroos, wanda ya zura a raga daf da za a tashi daga fafatawar.
Tuni dai Barcelona ta lashe kofin La Liga na bana kuma na 27 jimilla.
Kawo yanzu an buga wasa 370 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, an kuma ci kwallo 927.
Wasannin da za a buga a ranar karshe a La Liga:
- Real Mallorca da Rayo Vallecano
- Osasuna da Girona
- Real Madrid da Athletic Bilbao
- Real Sociedad da Sevilla
- Villarreal da Atletico Madrid
- Real Betis da Valencia
- Celta Vigo da Barcelona
- Espanyol da Almeria
- Real Valladolid da Getafe
- Elche da Cadiz